✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NDLEA ta gano gonar wiwi a Kano

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta gano wata makekeiyar gona da ake noma tabar wiwi a Unguwar Wailari…

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta gano wata makekeiyar gona da ake noma tabar wiwi a Unguwar Wailari da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Da yake  jawabi ga manema labarai Kwamandan Hukumar a Kano Dokta Ibrahim Abdul ya ce hukumar ta kuma kaddamar da wani shiri da ta yi wa lakabi da “sharar miyagun kwayoyi” inda ta kama mutum 280 da ake zargi da tu’ammali da miyagun kwayoyi cikinsu har da wadanda suke yi wa hukumar sojan gona.

“Wannan karo mun kaddamar da wani shiri na sharar miyagun kwayoyi. Wannan samame ya haifar da kama mutum 280 wadanda duk suna nan a tsare.  Kuma mun kama kwayoyi da suka kai tan 1248.537 Haka kuma mun kama wadansu da suke zuwa da sunan ma’ikatanmu ne suna karbar kudi a hannun jama’’a. A ranar 31 ga watan Maris kuma muka kama wata gonar wiwi mai girma a Unguwar Wailari a nan Kano.”

A cewarsa hukumarsu tana daukar duk matakan da suka kamata wajen kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi a fadin jihar.

Ya ce hukumar tana sane da wuraren da suka yi kaurin suna kan hada-hadar miyagun kwayoyi wadanda suka hada da Gandun Albasa da  Kofar Nasarawa da cikin Kwalejin Rumfa da karkashin gadar shatale-talen Titin Maiduguri da filin wasa na Unguwar Tudun Wada da ke birnin Kano.

Wadansu daga cikin wadanda aka kama sun bayyana yadda suka fada hannun Hukumar NDLEA, inda suka ce sun yi da-na-sanin abin da suka aikata

“Ni mutumin Katsina ne an kama ni da kwayar taramol amma ban ji dadin hakan ba. Kuma insha Allahu ba zan sake aikata haka ba,” inji daya daga cikinsu.