✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NDLEA ta kama masu tu’ammali da miyagun kwayoyi 95 a Ebonyi

Hukumar Yaki da masu Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama manyan dillalan tabar wiwi da masu shanta 95 a cikin wata 10…

Hukumar Yaki da masu Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama manyan dillalan tabar wiwi da masu shanta 95 a cikin wata 10 da suka gabata. Baya ga haka ta kwace miyagun kwayoyi da suka kai nauyin kilo 350 daga hannunsu.
Kwamandan Hukumar NDLEA na Jihar Mista Ralph Igwenagu ne ya tabbatar wa manema labarai haka a Abakaliki, inda ya ce sun kuma gyara halin mutum 40 da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi.
Da yake karin haske game da kamen Kwamanda Ralph ya ce “Zuwa yanzu kotu ta yanke wa mutum 10 daga cikin wadanda suka kama hukunci, kuma wasu 30 ana kan yin shari’arsu, sai 15 ana bincike game da su.”
Ya dora alhakin lalacewar matasa a halin yanzu kan shan miyagun kwayoyi, yayin da iyaye ba su son a rika fadin laifinsu. Ya hori iyaye su rika tsawatar wa ’ya’yansu domin hukumarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen damke duk wani mai lafi ko gagararre ba.