✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar SEMA ta kai dauki ga jama’ar da aka kai wa hari a Kudancin Kaduna

Hukumar Bayar da Agajin Gagawa ta Jihar Kaduna (SEMA) ta kai wa jama’ar da harin wadansu ’yan bindiga ya rutsa da su a Gundumar Zangan…

Hukumar Bayar da Agajin Gagawa ta Jihar Kaduna (SEMA) ta kai wa jama’ar da harin wadansu ’yan bindiga ya rutsa da su a Gundumar Zangan da ke Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna.

Da take mika tallafin ga Shugaban Karamar Hukumar, Shugabar  Hukumar SEMA, Hajiya  Maimunatu Asabe Abubakar ta ce bisa la’akari da abubuwan tausayin da suka faru da halin da wadanda harin ya shafa suke ciki musamman mata da kananan yara ya sa hukumar ta yi gaggawar kawo dauki don saukaka musu halin da suka tsinci kansu a ciki.

Hajiya Maimuna ta bayyana harin a matsayin abin takaici, inda ta yi kira ga mutanen yankin su zauna lafiya da junansu duk da irin bambancin addini da kabila da suke da shi.

Da yake jawabi bayan karbar kayayyakin, Shugaban Karamar Hukumar Dokta Katuka Ayuba Bege ya yaba wa Hukumar SEMA bisa ga abin da ya bayyana da daukin gaggawa a lokacin da ya dace, inda ya yi alkawarin mika kayayyakin ga jama’ar da abin ya shafa.

Ya ce karamar hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta hada kai da Kwamitin Zaman Lafiya na Jihar Kaduna don shiga tsakani don samun kyakkyawa fahimtar juna a tsakanin mutanen Ganawuri da ke Jihar Filato da al’ummar Fulani da Attakat da ke Zangan a Jihar Kaduna.

Kayayyakin da aka raba sun hada da katifu da barguna da gidajen sauro da buhunan shinkafa da manja da katan-katan na taliyar Indomi da sauransu.