✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Zabe ta fadi dalilan kai zaben qananan hukumomin Kano watan Mayu

Hukumar Zabe ta Jihar Kano ta bayyana dalilan da suka sanya ta tsayar da ranar 17 ga watan Mayun badi a matsayin ranar da za…

Hukumar Zabe ta Jihar Kano ta bayyana dalilan da suka sanya ta tsayar da ranar 17 ga watan Mayun badi a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben qananan hukumomin jihar.

Tun lokacin da Shugaban Hukumar Dokta Sani Lawan Malumfashi ya bayyana ranar 17 ga watan Mayun badi a matsayin ranar da za a gudanar da zaben qananan hukumomin, masu ruwa da tsaki ke ta sukar lamarin inda suke ganin akwai lauje cikin nadi.
Kwamishinan Hukumar Mmi kula da harkokin watsa labarai Alhaji Idris Isma’il Rimin Gado ya ce hukumar ta sanya wannan lokaci ne tare da fitar da jadawalin yadda zaben zai kasance don a ba jam’iyyu isasshen lokacin da za su shirya tunkarar zaben.
Shugaban wata qungiyar yaqi da cin hanci daga tushe (Grassroot Anti-corruption Awareness Network Initiatibe, GACANI) da ta yi ta kai-kawo don ganin gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da zaben qananan hukumomi a jihar wadda har ta shirya yin zanga-zanga a ranar 28 ga watan jiya domin tilasta wa gwamnati ta gudanar da zaben, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce akwai abin zargi a cikin jadawalin da hukumar ta fitar.
Magaji Rimin Gado wanda Mataimakin Shugaban Qaramar Hukumar Rimin Gado ne a lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ya cewa, “Za mu tuntubi lauyoyinmu a kan haka don daukar mataki na gaba. Haka kuma muna son qarin bayani game da aikin da hukumar za ta yi daga nan zuwa watan Disamba, don ba mu gamsu da dalilan da ta bayar game da sanya zaben a watan Mayun badi ba,” inji shi.