✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahimobic ya fara tunanin komawa Madrid

dan kwallon gaba a kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Zlatan Ibrahimomib ya fara tunanin komawa kulob din Real Madrid da ke…

dan kwallon gaba a kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Zlatan Ibrahimomib ya fara tunanin komawa kulob din Real Madrid da ke Sifen don hadewa da tsohon kocinsa Carlo Ancelotti kafin a fara kakar wasa ta bana.
Jaridar La Gazzetta dello Sport da ke Sifen ta ce, dan kwallon mai kimanin shekara 31 ya shaku sosai da koci Ancelotti kuma bai gamsu da sabon kocin PSG na yanzu Laurent Blanc ba.
Rahoton ya kara da cewa, dan kwallon ya amince kulob din Madrid ya zaftare albashin da ake biyansa a PSG muddin ya amince ya koma Sifen.
Jaridar Daily Star ta kalato cewa tuni kulob din Manchester City da na Chelsea da ke Ingila suka nuna sha’awarsu a kan dan kwallon, amma ya nuna ba ya sha’awar komawa Ingila sai dai kulob din Madrid da ke Sifen inda tsohon kocinsa Carlo Ancelotti ya zama sabon koci.
Tun bayan da kulob din PSG ya sayi Edison Cabani a makon jiya Ibrahimobic ya nuna aniyarsa ta barin kulob din.