Search
Subscribe
Idan ’yan siyasa ba su tafi da matasa ba akwai matsala – Tilde

Kwamared Aminu Sale Tilde

Idan ’yan siyasa ba su tafi da matasa ba akwai matsala – Tilde

Shugaban Majalisar Matasa ta Jihar Bauchi Kwamared Aminu Sale Tilde, ya ce matukar ’yan siyasar kasar nan ba su tafiya da matasa, sun sanya su a cikin harkokin siyasa ba, za a ci gaba da samun matsala a siyasar Najeriya.

Kwamared Aminu Tilde ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, inda ya ce matasa su ne suke da lafiya da karfi da kuruciyar da za su jagoranci mulkin jama’a cikin nasara, sabanin mutanen da suka fara manyanta.

“Saboda haka muna goyon bayan duk wani matashi kuma muna kira ga matasa a duk lokacin da aka ba su mukami su yi kokari su kwatanta adalci. Idan har ba za a ba su dama su yi adalci ba, su ajiye wannan mukami da aka ba su,” inji shi.

Ya ce su a matsayinsu na matasa za su mara wa duk wani matashi da zai zo da abubuwan da za su toshe duk hanyar cin hanci da rashawa a Jihar Bauchi da kasa baki daya.

Sai ya yi kira ga matasa su ci gaba da tsayawa wajen ganin an ci gaba da aikata gaskiya a kasar nan.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin