✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina nan ban mutu ba-Sani SK

Fitaccen jarumin nan na Kannywood, Sani SK wanda ya fi yin fice a wasannan barkwanci ya musanta jita-jitar da ake yada wa cewa ya mutu.…

Fitaccen jarumin nan na Kannywood, Sani SK wanda ya fi yin fice a wasannan barkwanci ya musanta jita-jitar da ake yada wa cewa ya mutu.

A jiya ne aka wayi gari da jita-jitar a kafafen sadarwa na Facebook da Instagram da Tiwita, inda ake ta yawo maganganun cewa jarumin ya rasu.

Amma da safiyar yau Talata, Jarumi Abba Elmustafa ya sanya hotonsa tare da Sani SK inda ya bayyana cewa lallai Sani SK yana, kuma yana samun sauki a rashin lafiyar da ke damunsa.

Hakanan ma a wani bidiyo da wani ya sanya a facebook tare da jarumin, an nuna Sani SK yana kwance, inda yake bayyana cewa yana nan bai mutu ba.