Da Dumi Dumi

Ina Za Mu A Nes Lebul? (1)

Ranar Laraba da ta wuce , 29 ga watan Mayu, 2019 ne aka rantsar da Shugaba Buhari a matsayin Shugaban kasa a karo na biyu, bayan da ya kammala shekara 4 na farko daga shekarar 2015. Tun kafin a rantsar da shi da sauran gwamnoni an riga an ga yadda shekara hudu da suka wuce suka kasance a Najeriya, ana kuma da hasashe na yadda shekara hudu masu zuwa za su kasance, wato abin da gwamnati da wasu ke kira Nes Lebel na shugabanci daga gwamnatin APC da Shugaba Buhari.

A yau ba nes lebel din zan fuskanta kai tsaye ba, domin ba a fara ba sosai, bare mu gane dawan garin. Abin da zan yi shi ne in bi da mu bisa turbar tarihin tsarin siyasa da mulki da dimokuradiyya da aka yi a aijeriya a baya da irin yadda tarihin ya gina abin da muke gani yanzu da kuma tunanin yaya za a iya shawo kan irin wadannan matsaloli in mun tunkare su nan gaba, a nes lebel din. Yin haka na da muhimmanci, domin daga inda saniyar gaba ta sha ruwa ake gane zurfin ruwa.

Bincike-bincike da nazarce-nazarce da aka dade ana gudanarwa kan yadda al’ummu ke ginuwa, musamman a kasashe masu tasowa daga shekarun 1950 suna tafe ne da nasu kamannu daban-daban. Akwai masu kallon ginin al’ummar ta fuskar yanayin jan ra’ayin jama’a don su saje a matsayin tsintsiya madaurinki daya, a maimakon a tsaya a warwatse ta yadda abokan gaba ko adawa za su iya samun galaba a kan su da sauri. Misalin irin wannan tsari ne aka samar a kasashe da tsarin mulkinsu na gargajiya ne ko kuma na zamani, inda shugabanci ke fadawa a hannun masu gari ko iyayen kasa ko kuma jam’iyyun siyasa, wannan ra’ayi shi ke tashe a fannin nazarin zamantakewa.

Sobada haka duk tsarin da bai da wata madogara ko wata majalisa da za ta kula da yadda ake samar da dukiya a kasar da yadda ake raba ta, to wannan tsari zai kasance tamkar tsarin mulkin wawaso ne, kowa ya dauki rabonsa. Wannan ne ya sa ko inda ake da tsarin mulki da jam’iyyun siyasu, tsayayyu, murdiya da cin zabe ta hanyar zurmuke, hanyoyi ne na amsar mulki da kuma danne muryar adawa da kokarin tabbata bisa mulkin, ko da jama’a ba sa so. A irin wannan tsari, adawa takan yi tsanani da zafi domin ba wanda ke son a kada shi a zabe, musamman a yawancin kasashen Afirka, wannan ne kan sa wasu kokowa, suna ganin cewa dimokiradiya a irin wannan tsari ba ta zauna da gindinta ba, mulkin kare ’yanci da ci gaban jama’a a wannan tsari ba shi aka sa gaba ba, balle ma a damu da shi.

Duk da cewa ra’oyoyi sun bambanta dangane da irin wannan halayya, abin da ke da muhimmanci bai wuce haka lallai na faruwa ba, wasu na tsine wa wadanda suke gallaza musa, wasu na murna ganin cewa mulki ya fado hannunsu ko da kuwa wannan ba zai taimaka wajen ci gaban dimokiradiya ba, balle uwa-uba ginuwar tattalin arzikin }asa. A kula ci gaban }asa da kyakkyawan tsarin dimokira]iya abubuwa ne da yawancin jama’a ke }ishirwa su, musamman a }asashe masu tasowa. Rashin su kuwa babbar matsala ce ga rayuwar al’umma.

ADVERTISEMENT

Yawancin kasashen Afirka sun shigo turbar zamananci da muke gani yanzu daga mulkin gargajiya, sai dai an samu wadansu ’yan canje-canje. A wadansu sassan an sha ba-ta-kashi da wadanda ba su son zamananci, sun fi son a ci gaba da abin da aka gada. Bisa irin wannan tunani ne, wasu masu mulki suka fara tunanin yadda za su dawwama bisa mulkin don jin dadin kansu, ko da kuwa sauran jama’a na cikin ukuba. Irin wannan tantagaryar rashin kunya da kwace da danniya rana tsaka ya sa wasu gungun jama’a ke bijerewa, wasu ke neman canji ko da gora, wasu ke ganin cewa bin matakin yin adawa tamkar addini ne, ba kuma za su daina ba, a wannan lokaci wanda aka danne bai damu da ya tunkari tankunan yaki ba, in dai hakan ne kurum zai sa ya kasance da ba bawa ba a cikin kasarsa, kamar yadda marigayi Malam Aminu Kano,ya sha fada.

Ba za a iya gane haka ba, musamman dangane da irin abin da ke faruwa a irin wadannan kasashe masu tasowa irin Najeriya har sai an fahimci  da tattauna yanaye-yanaye da sauye-sauyen fuskar da mulki ke dauka a zanguna daban-daban a rayuwar kowace al’umma, musamman a tsarin mulki irin na zamani da hada-hadar siyasa. Yin haka ya sa dole an tabo yadda aka samar da kasar Najeriya da yadda ta ginu tun daga zangon gargajiya zuwa tsarin jari-hujjar ’yan-ba-ruwanmu da take gudanarwa a halin yanzu, sa’annan a kuma dubi yadda aka samar da jama’a tsakanin masu shi da marasa shi, wanda ya jawo tashin-tashina tsakanin yawancin jama’a, wata sa’a da zage-zage da buge-buge da kuma kashe-kashe. Za a tsokano wannan yanayi ne domin mu fahimci dalilan da suke sa wadansu gungun jama’a ke amfani da karfin tuwo a wajen gudanar da mulki a maimakon lalama da ban magana. Yin haka zai taimaka wajen zayyana hoton rayuwar dangantakar da ke tsakanin gwamnati da wadanda take mulka da kuma fiddo fili damar da jama’a ke da ita ta mika kai ko kuma bijirewa a cikin irin wannan tsari.

 Za Mu Ci Gaba

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya