✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jakadan Birtaniya a Amurka sakarai ne – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya kira Jakadan Birtaniya a Amurka Kim Darroch da “sakarai” a wani yunkuri na watsi da rahoton da Jakadan ya bayar…

Shugaban Amurka Donald Trump ya kira Jakadan Birtaniya a Amurka Kim Darroch da “sakarai” a wani yunkuri na watsi da rahoton da Jakadan ya bayar kan Trump cewa shi “dakiki ne” kuma “mara kwarewa”.

Shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na Twitta cewa, “Jakadan Birtaniya  a Amurka wanda ba a maraba da shi, ba wani mutum ba ne da aka damu da shi.”

Shugaban na Amurka ya ce Darroch, wanda shi ne Babban Jami’in Diplomasiyyar Birtaniya a Washington tun shekarar 2016, “kamata ya yi ya damu da magana a kan kasarsa da kuma Firayi Minista May, musamman kan tattaunawar ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai, wadda ta kasa kammalawa, kuma kada ya ji haushin sukar da na yi kan yadda aka yi shirme wajen gudanar da al’amarin.” Kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Trump ya ci gaba da cewa, “Na fada wa Theresa May yadda za ta cimma yarjejeniyar, amma ta bi wata hanyarta ta wauta, wanda hakan ya sa ta kasa shawo kan lamarin. Ni ban ma san Jakadan ba, amma na ji an ce sakarai ne mai ji-ji-da-kai. Amma dai abin murnar shi ne Birtaniya ta kusa samun sabon Firayi Minista,” inji Trump. Ya kara da cewa, “duk da cewa na ji dadin ziyarar da na kai Birtaniya watan jiya, na fi jin dadin ziyarar sarauniya.”

Jim kadan bayan wadannan kalamai, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Jeremy Hunt ya mayar da martani, inda ya yi kashedi ga Trump cewa kalamansa da Birtaniya na cike da “rashin mutunci kuma ba su dace ba.” Hunt ya ce idan har ya samu nasarar zama Firayi Ministan Birtaniya bayan May ta sauka, zai sake tura Darroch ne ya ci gaba da zama Jakadan Birtaniya a Amurka din.

Shi dai wannan rikicin ya biyo bayan fallasa wasu sakonnin sirri na diflomasiyya da Amurka ke zargin Jakadan Birtaniyya da hannu a ciki, wanda hakan ya sa Trump ya ce Amurka ba za ta sake yin mu’amala da shi ba a matsayin wakilin Birtaniya a kasar.

Tun farko Birtaniyya ta bayyana rashin jin dadinta bisa wannan matsalar, duk da cewa Firayi Minista Theresa May ta nuna goyon bayanta dari bisa dari ga Jakada Kim Darroch.