✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigawa ta kasafta Naira biliyan 152 a badi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kasafta kashe Naira biliyan 152 da miliyan 152 da dubu 92o a badi. Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kasafta kashe Naira biliyan 152 da miliyan 152 da dubu 92o a badi. Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana haka a ranar Talata a lokacin da yake gabatar da kundin kasafin kudin a gaban Majalisar Dokokin Jihar.

Ya ce kasafin kudin na badi zai fi mayar da hankali ne wajen ilimi da lafiya da kula da tsabtar muhalli da bai wa bangaren aikin gona muhimmanci.

Ya kara da cewa kaso mafi tsoka gwamnatin za ta kashe ne wajen gyaran makarantu da gina sabbin ajujuwa da sayen kayan koyo da koyarwa da kuma kujeru da teburan dalibai da malamai.

Gwamna Badaru ya ce kananan hukumomi jihar su kuma kasafin kudin na badi za su kashe kimanin Naira biliyan 20.18, inda bangaren ayyuka a kananan hukumomin zai dauki kaso mafi girma.

Gwamna Badaru ya ce daga cikin kashi goma na kasafin kudin na badi, bangaren lafiya da harkar noma da ilimi ne za su dauki kashi biyu da rabi. Ya ce an samu karin Naira biliyan uku a kasafin na badi sama da kasafin kudin bana.

Gwamnan ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen gina dan Adam ta hanyar taimaka wa al’umma don inganta rayuwarsu.

A kasafin kudin, gwamnatinsa ta ware Naira biliyan 18.3 da nufin kammala ayyukan hanyoyin mota da ta fara, tare da aiwatar da sababbin hanyoyi da nufin inganta hanyoyin sufuri a jihar.

A jawabin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Idris Garba Kareka ya ce za su yi wa kasafin kudin nazari cikin sauri tare da amincewa da shi ba tare da bata wani lokaci ba.

Ya ce cikin mako uku majalisar za ta kammala nazari kan kasafin kudin kuma ta mayar wa Gwamnan domin ya rattaba hannu ya  zama doka don gwamnatin jihar ta samu ikon yi wa talakawa da suka zabe ta ayyukan da ta dauki alkawarin yi.