✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jigawa za ta ba da Naira miliyan 13 don laccar tunawa da Malam Aminu Kano

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da Naira miliyan 13 ga Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya da Horarwa ta Malam Aminu Kano domin tallafa mata wajen gudanar da…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba da Naira miliyan 13 ga Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya da Horarwa ta Malam Aminu Kano domin tallafa mata wajen gudanar da laccar tunawa da Malam Aminu Kano ta bana.
Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ne ya bayyana tallafin a lokacin da shugabannin cibiyar a karkashin jagorancin daraktan cibiyar Farfesa Muhammad dahiru Suleiman suka wa Gwamnan ziyarar girmamawa a Dutse.
Gwamna Lamido ya ce Malam Aminu Kano ya bayar da gagarumar gudunmawa a fagen gwagwarmayar siyasar kasar nan, musamman a fagen kwato hakkin talakawa, inda ya ce ta hanyar koyarwarsa da sadaukar da kansa rayuwar talakan Arewa ta inganta.
Ya ce gwamnatin Jihar Jigawa a shirye take ta hada kanta da duk wani yunkuri na tunawa da marigayin gogaggen dan siyasar.
Gwamna Lamido ya nuna damuwa kan “miyagun halayen da ’yan siyasa da ma’aikatan yanzu suka tsoma kansu a ciki alhali sun ci gajiyar ’yanto talakawa da Malam Aminu Kano ya yi.”
A nasa jawabin Farfesa dahiru Suleiman ya gode wa Gwamna Lamido kan wannan tallafi inda ya ce taken laccar ta bana shi ne: “Siyasar Jam’iyya da kokarin Gudanar da Zabe Na kwarai a Najeriya,” kuma Gwamnan Jihar Edo Kwamared Adams Oshiomhole ne zai gabatar da ita.