Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Jose Mourinho ya amince da daurin shekara daya a gidan yari

Tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho ya amince da daurin shekara daya a gidan yari a Spain saboda kama shi da laifin kin biyan haraji.

Da wahala ya yi zaman gidan yarin saboda ba kasafai kasar Spain ke matsa wa kan mutum ya je gidan kason ba idan daurin da aka yi masa bai kai shekara biyu ba.

ADVERTISEMENT

Spain ta zargi kocin wanda dan asalin kasar Portugal ne da kauce wa biyan haraji na Fam miliyan 3.3.

Baya ga daurin je-ka-ka-gyara-halinka, tsohon kocin zai biya tarar Fam miliyan 2.

ADVERTISEMENT

BBC ya ruwaito cewa laifuffukan da aka same shi da aikatawa sun shafi rashin bayyana kudin da ya samu daga tallar hotunansa lokacin da yake kocin Real Madrid tsakanin shekarar 2011-2012.

An zarge shi da bude hanyoyin kasuwanci daban-daban a Tsibiran Birtaniya na Birgin Islands da wasu wurare da ke tallata hotunansa.

Masu shigar da kara sun ce ya yi hakan ne da niyyar kauce wa biyan haraji.