Joseph Yobo ya zama Mataimakin Kocin Super Eagles

Hukumar Kwallon Najeriya, NFF ta zabi tsohon dan wasan Najeriya, kuma tsohon kyaftin din kasar, Joseph Yobo a matsayin Mataimakin Kocin ’yan kwallon Najeriya, wato Super Eagles.

Yobo zai maye gurbin Imama Amapakabo a matsayin, inda zai ci gaba da aki tare da Gernot Rohr.

Tsohon dan wasan, ya buga wa kungiyoyi da dama a ciki da wajen Najeriya, ciki har da Everton, inda ya fi yin suna har ya kai ga zama kyaftin.

Ya buga Gasar Kofin Afirka sau 6, a shekarun 2002 da 2004 da 2006 da 2008 da 2010 da 2013.

Shi ne kyaftin din Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe Gasar Kofin Afirka a shekarar 2013.

ADVERTISEMENT

A rukunin Super Eagles, Joseph Yobe ya bugawa Njeriya wasa 100. Ba ya ga wasannin da ya buga wa Najeriya a wasannin ’yan kasa da shekara 20.

A shekarar 2001 ne ya fara bugawa Super Eagles, inda ya taka leda a wasan Najeriya da Zambia a garin Chingola a watan Afrilun.

Ya kuma halarci Gasar Kofin Duniya sau uku, a shekarun 2002 da 2010 da 2014.

Share