Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Kada ku bata ayyukanku (2)

Kada ku bata ayyukanku (2)

Daga Sheikh Ibrahim bin Salih Al-Ajlan

Masallacin Sheikh Bin Baz Riyad, Saudiyya 

Kuma duk wanda ya yi ridda ta hanyar aiki ko ta furuci ko i’itikadi, hakika aikinsa ya baci. Allah Madaukaki Yana cewa Yana mai jingina ridda da hasara: “Kuma wanda ya kafirta da imani, to, lallai ne aikinsa ya baci, kuma shi a Lahira yana daga cikin masu hasara.” (Ma’ida:5).  

Ya ku muminai! Idan jiji-da-kai ya samu gurbi a zuciyar mutum sai kuma ya rika alfahari da ayyukansa, kuma sai ya rika jifar sauran mutane masu aikata zunubi wadanda suka gaza da cewa ba su cancanci rahamar Allah ko gafararSa ba. Wannan jifa ce a cikin duhu da shiga gonar Allah. Wanda yake aikata wannan mugun aiki hakika shi ma ya zo ga kofar bata ayyukansa. Muslim ya ruwaito a sahihinsa daga Jundub (RA) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai wani mutum ya ce: “Wallahi Allah ba zai gafarta wa wane ba!” Sai Allah Mabuwayi ya ce: “Wane ne yake shiga gonaTa cewa ba zan gafarta wa wane ba? To na gafarta wa wanen, kai kuma na bata ayyukanka!”

Daga cikin ayyukan da suke jawo rusa lada, akwai bari (ko wasa da) Sallar La’asar. Buhari ya ruwaito a sahihinsa daga Buraida (RA) cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya bar (ya yi wasa da) Sallar La’asar hakika aikinsa ya baci.”

Ibn kayyim (Rahimahullahu) ya ce: “Barin nau’i biyu ne: Bari gaba daya ba ya yin Sallar kwata-kwata, to wannan yana bata aikinsa gaba daya. Sai kuma bari ayyananne a wata rana ayyananniya. To wannan yana bata aikinsa na wannan ranar. Wato baci na gaba daya yana tafiya tare da bari na gaba daya. baci na ayyananne yana tare da bari ayyananne.”

Ya ku Musulmi! Idan aka zo wajen auna i’itikadi a mizani, sai aka iske gaskiya ta cakuda da camfe-camfe, sai mutum ya bace daga hanya madaidaiciya. Za a ga wani yana neman yadda zai kubuta ko ya samu lafiya ta hanyar ziyartar bokaye da masu shu’umci. Yin haka aukawa ne ga babbar kofa daga cikin kofofin kin karbar aiki. Annabi (SAW) yana cewa: “Duk wanda ya zo wurin boka kuma ya tambaye shi kan wani abu, ba za a karbi sallarsa na kwanaki arba’in ba.” Muslim ya ruwaito shi.

Wannan fa kawai a kan ya tambaye shi ne, ba a zo kan batun gaskata shi ko karbar maganarsa ba. Idan ya gaskata shi ko ya karbi maganarsa, to ya fice daga Musulunci ne gaba daya. Domin Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda duk ya je wurin boka ko mai duba kuma ya gaskata shi cikin abin da ya fada, hakika ya kafirta da abin da aka saukar ga Annabi Muhammad.” Ahmad da wadansu suka ruwaito, kuma Hadisi ne hasnun. 

Gori dabi’a ce ta kaskanci, abar zargi kuma tana bata ayyuka. Sannan ba dabi’ar masu mutunci da karimci ba ne. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku bata sadakokinku da gori da cuyatrwa…” (Bakara:264).

Hankali ni’ima ne na Ubangiji da ba a kwatanta shi da kudi, a duk lokacin da mutum ya butulce wa wannan ni’ima ya bata hankalinsa da kansa, hakika ya aikata babban laifi kuma ya kai kansa ga kofar kin amsar aikinsa. Ya zo a cikin Hadisi cewa: “Wanda ya sha giya ba za a karbi aikinsa na kwana arba’in ba.” Ahmad da Nisa’i suka ruwaito kuma Ibn Hibban ya inganta shi.

Har wa yau daga cikin laifuffukan da suke bata ayyuka na kwarai, akwai kaurace wa iyaye da rashin kyautata musu da karyata kaddara. Annabi (SAW) ya ce: “Mutum uku Allah ba zai karbi wani aiki daga gare su ba: Mai kaurace wa iyayensa da mai gori da kuma mai karyata kaddara.” Ibn Abu Asim da dabarani suka ruwaito kuma Munzari da Albani sun ce hasanun ne.

Daga cikin miyagun ayyuka ababen ki da suke bata ayyuka akwai abin da Annabi (SAW) ya ambata a cikin fadinsa: “Mutum uku sallarsu ba ta wuce kunnunwansu: Bawa gudajje har sai ya koma ga ubangidansa da matar da mijinta ya kwana yana fushi da ita da kuma shugaban mutane da suke kin sa.” Tirmizi ya ruwaito kuma Hadisi ne hasnun.

Allah Ya yi mana albarka ni da ku a cikin Alkur’ani da Sunnah, kuma Ya sanya mu daga cikin masu bin Shugaban Aljanu da Mutane. Ina neman gafarar Allah a gare ni da ku daga dukan zunubi da sabo, ku tuba gare Shi kuma ku nemi gafararSa, Lallai ne Shi ga masu tuba Mai yawan gafara ne.

Huduba ta Biyu:

Bayan haka ya ku ’yan  uwa a cikin imani! Hasara takan kai magaryar tukewa, radadi ya kai karshe idan aka ce kyawawan ayyukan bawa su watse, kuma ladansa ya fada cikin ma’aunin wanda ba shi ya yi aikin ba. Wannan shi ne muguwar hasara da tabewa ta hakika da Annabi (SAW) ya yi mana gargadi a kai. Shi ne halin mutumin da ya yi aiki ya sha wahala ya gaji, ya yi Sallah da Azumi da Zakka, amma sai ya tafi Lahira dauke da tulin zalunci da cuta. Ya ce: “Hakika ya zagi wannan, ya yi kazafi ga wancan, ya ci dukiyar wannan ya zubar da jinin wancan, ya kuma doki wannan. Sai a dauki kyawawan ayyukansa a biya wannan da wancan. Idan kyawawan ayyukansa suka kare kafin ya biya abin da ke kansa, sai a dauko zunubansu a jibga masa a tura shi cikin wuta!” Muslim ya ruwaito.

A karshe ya ku ma’abuta imani! Ku sani lallai masu tsare ayyukan kwarai suna nuni ne ga tabbatuwar takawa da gaskiyar imani da Aljannar Mai rahama. Kuma ana gadar da shi ne ga wanda ya yi aiki kuma ya tsare aikinsa daga baci. “Kuma aka kira su cewa: “Waccan Aljanna an gadar da ku ita, saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.” (A’arafi:43).

Ya bayin Allah! Wadancan su ne wani yanki na munanan ayyuka da suke bata kyawawan ayyuka, don haka ku lura da su kuma ku kiyaye su, ku fahimce su ku guji aikata su.

Hamadani Abu Firasu yana cewa: 

“Na san sharri ne ba don in yi sharri ba, 

sai domin in kauce masa. 

Kuma wanda bai san sharri ba daga cikin mutane sai ya auka cikinsa.”

Ya Allah Ka kara tsira da aminci ga Shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa.