Daily Trust Aminiya - Kafa Rundunar Amotekun ya haifar da zaman dar-dar da cece -k
Subscribe

Motocin sintiri da jami’an rundunar Ametokun. Hotunan Sama Daga Hagu: Alhaji Kabir Labar da Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu da kuma Alhaji Muhammadu Musa Maitakobi

Kafa Rundunar Amotekun ya haifar da zaman dar-dar da cece -kuce

A makon jiya ne gwamnonin yankin Kudu maso Yamma da suka hada da jihohin Legas da Oyo da Ogun da Osun da Ondo da Ekiti suka kaddamar da wata rundunar tsaro ta musamman da suka sanya wa suna “Amotekun” wadda a cewarsu sun kafa ta ce domin karfafa harkokin tsaro a yankinsu.

Sai dai kuma sabuwar rundunar, wacce aka kaddamar a Ibadan, Jihar Oyo a ranar Alhamis din makon jiya ta bar baya da kura, inda wadansu ke goyon bayan samuwarta, wadansu kuma suke hangen rikidewarta zuwa rundunar ’yan sandan yanki. Wadansu daga cikin masu fada-a -ji a yankin Yamma sun yi gum da bakinsu kan wannan lamari.

Kafin kaddamar da rundunar sai da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Muhammed Adamu ya gana da gwamnoni shida na yankin, domin toshe hanyar yiwuwar rikidewar rundunar zuwa ta ’yan sandan yanki, bayan ga rundunar ’yan sanda ta kasa da tsarin mulki ya amince da ita.

Mai masaukin baki a wajen bikin kaddamarwar, Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo da Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredelu da mataimakan gwamnonin jihohin Osun da Ogun ne suka bayyana a wajen kaddamar da sabuwar rundunar ta musamman da aka sanya wa Rundunar Tsaro ta Yammacin Najeriya (Western Nigeria Security Network – WNSN), kuma aka yi wa lakabi da taken ‘Rundunar Amotekun’ (Rundunar Damisa), wacce za ta gudanar da ayyukan tsaro a yankin.

Gwamna Sanwo-Olu na Jihar Legas bai halarci bikin ba kuma babu wakilinsa. Rundunar wacce ta fara aiki bayan kwana daya da kaddamar da ita, an baje kolin sababbin motoci masu dauke da tambarin kowace jiha da jami’an rundunar sanye da rigar sarki ta aiki.

Mafi yawan jami’an rundunar mafarauta ne da gwamnonin suka amince su rike bindigar harbi-ruga amma ba a yarda su tsare wanda suka kama da zargin aikata wani laifi ba, sai dai su mika ga ’yan sanda mafi kusa da su.

Kungiyar Matasan Arewa  (NYCN) ta nuna rashin amincewa da bullar wannan runduna ta Amotekun, domin a cewarta, barazana ce ga tsaron kasa.

Cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar, Alhaji Isah Abubakar ya raba ga ’yan jarida, ya ce “Rundunar ta Amotekun a yankin Kudu maso Yamma, kungiya ce mai sanye da rigar Kungiyar Yarabawa Zalla ta OPC. Saboda haka muke kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin 6 da dukkan masu ruwa-da-tsaki, kada su amince da kafuwarta, domin barazana ce ga tsaron lafiyar kasa.”

Aminiya ta lura cewa da yawa daga cikin manyan sarakuna da manyan malaman addinai da wasu fitattun kungiyoyi a sashen ba su halarci bikin kaddamar da rundunar ba. Shugabannin hukumomin tsaro na ’yan sanda da soji da kwastam da na shigi-da-fici ba su halarci bikin ba, duk da cewa akwai yiwuwar aikin hadin gwiwa da aka ce za su yi da sabuwar rundunar ta Amotekun.

Amma cikin jawaban gwamnonin, sun tabbatar da cewa an kai ga matakin karshe na kaddamar da rundunar ce da amincewar dukkan sarakuna da malaman addinai da shugabannin al’umma da dukkan masu ruwa-da- tsaki kan tsaron lafiya da dukiyar jama’arsu da baki mazauna wannan sashe.

Shi kuwa Alhaji Muhammadu Musa Maitakobi, Shugaban Kungiyar Masu Motocin Sufuri ta Kasa (REATAN) kuma Mataimakin Sarkin Hausawan Kasuwar Duniya ta Alaba, wanda ya halarci taron kaddamar da Amotekun din, ya shaida wa Aminiya cewa Yarbawa na nema wa kansu mafita ce, maimakon su tsaya sai Gwamnatin Tarayya ta kai musu dauki. Ya ce tsarin tsaron na Amotekun abu ne da ke da bukatar kyakkyawar fahimta.

“Sun shaida mana dalilansu na fiddo da wannan tsari, inda suka ce sun yi ne domin kyautata yanayin tsaro a jihohinsu. Sun kuma shaida mana yadda ayyukan kungiyar za su kasance, cewa za su yi amfani da ’yan kungiyar ce da za su yi aikin ba da tsaro a yankunansu na asali. Wannan shi ne zai taimaka wa shirin domin sai da dan gari akan ci gari,” inji shi.

Shi ma Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu, Shugaban Kungiyar Hadaka ta Matasan Arewa, ya shaida wa Aminiya cewa su al’ummar Arewa mazauna jihohin Yamma  ba su fargabar kafa kungiyar tsaro ta Amotekun, domin yunkuri ne da al’ummar yankin suka yi na kare jihohinsu daga fadawa kalubalen tsaro da ake fama da su a wasu jihohin Arewa.

Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyyati Allah na jihohin Yamma, Alhaji Kabir Labar ya shaida wa Aminiya cewa ba su inkarin duk wani abin da zai kawo zaman lafiya, domin zaman lafiya shi ne ya fi komai. Sai dai ya ce bai kamata a ware wadansu jama’a da su ma ke zaune a yankin ba, idan ana maganar kyautata tsaro. Ya ce kamata ya yi a tabbatar da an samu kyakkyawar fahimta tare da tuntubar juna. “Tsoronmu da al’amarin shi ne, kada ya zamo an samu wata dama ta musgunawa ko tsangwamar wata kabila ko jinsi na al’umma,” inji shi.

Wadansu daga cikin ’yan Arewa mazauna Legas da Aminiya ta zanta da su, wadanda ba su so a ambaci sunansu, sun ce tsoronsu da shirin na Amotekun shi ne, kada a bai wa ’yan Kungiyar OPC damar ci gaba da musguna wa jama’a, kamar yadda suka yi a baya. Suka ce cikas din da za a iya samu shi ne, gwamnonin da suka yi yunkurin ba za su iya daukar nauyin mutanen da za a bai wa horon ba, don haka bai wa irin wadannan mutane makamai tamkar an ba su damar su yi tu’annati ne, domin su samu abin da za su dogara da shi.

Da yawa daga cikin al’ummar Yarbawan yankin sun nuna goyon bayansu, domin suna kallon shirin a matsayin wani abu da zai inganta tsaro a yankin kuma ya samar wa matasansu ayyukan dogaro da kai.

Shin ko yaya Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ke kallon wannan al’amari na Amotekun? Da kungiyar ke mayar da martani game batun, cewa ta yi ba a da bukatar rundunar tsaron yanki, domin kamar maimaita ce kawai na rundunonin tsaro da ake da su a kasa.

Sakataren Watsa Labarai na Kasa na Kungiyar ACF, Muhammad Ibarhim Biu ya hori gwamnonin Kudu maso Yamma su guji yin amfani da rundunar domin bukatar siyasa. Ya ce babu wani tabbaci da gwamnonin za su bayar da zai kwantar wa mutane da hankali, musamman mazauna yankin. Sannan ya bayyana rundunar a matsayin maimaita aikin da wadansu suke yi kuma abin da ba shi ake bukata ba.

“Game da batun nan, Kungiyar ACF na fargabar sanya siyasa a cikin lamarin da kuma tunanin dacewarsa da dokokin kasa. Sannan Kungiyar ACF tana matukar fargabar rikicin da abin zai haifar wajen gudanar da ayyukan rundunar, musamman tsakaninsu da ’yan sanda. Don haka ne ACF take gargadin kada a assasa rundunar tsaron da za a yi amfani da ita wajen siyasa, sannan a yi amfani da dukiyar kasa wajen lura da ita. Yawancin jihohi yanzu ba su iya biyan albashi da fansho,” inji shi.

Da yake magana kan yadda aiki ya yi wa jami’an tsaron Najeriya yawa, sai ya shawarci jihohin su hada hannu da Gwamnatin Tarayya wajen fitar da tsarin da doka ta amince da shi wajen samar da tsaro a yankinsu.

A nata bangaren, Gwamnatin Tarayya haramta rundunar tsaron ta Amotekun ta yi a farkon makon nan, inda a cikin wata sanarwa da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya fitar, ta bayyana rundunar a matsayin haramtacciya, lura da cewa, ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Mai magana da yawun Ministan, Dokta Umar Jibrilu Gwandu ya ce batun samar da tsaro da makami hakki ne da ya rataya kan Gwamnatin Tarayya. “Don haka wani bangaren kasa ko ma jihohi ba su da damar kirkirar nasu hukumomin tsaron kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima,” inji shi.

Ya nanata cewa kirkirar kungiyar wani laifi ne da ya saba wa doka, domin an yi tanadin jami’an tsaro na soji da na ’yan sanda da na ruwa da kuma sojin sama, wadanda su ne ke da alhakin tabbatar da tsaro a dukkan sassan Najeriya.

Ya ce jihohin sun yi gaban kansu ne ba tare da sun tuntubi ofishin Ministan Shari’a ba kafin daukar matakin kafa rundunar tsaron ta Amotekun.

Ko yaya gwamnonin yankin Kudu maso Yamma suka ji da wannan mataki na Gwamnatin Tarayya? Shugaban Gwamnonin, Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, a ta bakin mai ba shi shawara ta fuskar tsaro, Jimoh Dujomo ya gaya wa Aminiya cewa ya yi wuri tun yanzu ya ce zai maida martani kan batun haramcin.

Shi ma a nasa bangaren, Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a yayin wani taron manema labarai, cewa ya yi gwamnonin yankin za su zauna domin duba batun haramcin nan ba da jimawa ba.

Kafin wannan sanarwa ta Gwamnatin Tarayya, wadansu ’yan Najeriya da dama sun goyi bayan bijiro da kungiyar da suke ganin za ta taimaka wajen yaki da matsalolin tsaro a shiyyar Yamma, cikinsu kuwa har da sanannen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka. Sai dai wasu rahotanni sun ce al’ummar Yarabawa za su kalubalanci matakin haramta rundunar.

Ita kuma Kungiyar Dattawan Kudu da na Midil Belt, fatali ta yi da matsayin Gwamnatin Tarayyar na haramta rundunar ta Amotekun. A wata sanarwa dauke da sa hannun Yinka Odumakin (Kudu maso Yamma) da Janar CRU Iherike (Kudu maso Gabas) da Sanata Bassey Henshaw (Kudu maso Kudu) da Dokta Isuwa Dogo (Midil Belt), sun ce matsayar Babban Lauyan Gwamnatin ‘cin amanar ofishinsa ne.’

Sun bukaci Minista Malami ya bayyana musu karara kan “Me ya sa Amotekun ta zama haramtacciya amma Hisbah kuma ta halatta? Sa’annan ya fito ya fada mana dalilin da ya sa Sibiliyan JTF ta zama halatacciya a Arewa maso Gabas da ake yaki, yayin da a Zamfara da Katsina kuma ba ma yakin ake yi ba? Amotekun ce kawai haramtacciya a wajensa? Wannan ne lokacin da ya kamata a bayyana mana cewa ko muna rayuwa ne cikin nuna bambanci tare da dokoki mabambanta a kasa,” inji su.

texem
More Stories