✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kagen kunduge kwangen kwage

Salallamin sauke Salami Sallamar mai mukami Babu daukar makami Watsattsake ne da alkalami A dai kwace damin burgami   Kotun kwaram-kwandon Tuhumar boye matsabbai a…

Salallamin sauke Salami

Sallamar mai mukami

Babu daukar makami

Watsattsake ne da alkalami

A dai kwace damin burgami

 

Kotun kwaram-kwandon

Tuhumar boye matsabbai a lungu

Sai ta dauro mutum a kugu

Kwaramniyar shan dundun

Dudun-dundun

 

Salalar salular sili-tili

Santalar Santali

Subul da bakan tonon silili

Shaci-fadin rashin hankali

Shashancin shari’ar shagali

 

Masu dibar dukiya sui fatali

Su daure mai kin biyan jangali

Komarsu na walwali

Nau’ukan kifaye akai wa fasali

Batun ga ba aiki da hankali

 

An yi Audu Awon-doka

An yi Adoke Doka

Makalutun Malami

Sai ka kara kaimi

Don ka da kowa ya koka

 

Kagen kunduge kwangen kwage

Dungun dudduge

Durgu ya dage

Dukiya an kange

Kariyar kwandon Barau aka buge

 

Bera na tsoron mage

Sauro ya sagale a sange

Batun ingarma babu kage

Mai kiren karya ya doge

Cincin karfi ya daddage

 

Laulayin doka

Tabargaza an tafka

Takun turka-turka

An yi kiki-kaka

Mai shari’a na bin Dan-wanka

 

Bambamin baka

Bankade-bankaden bukka

An dai samu baraka

Rashin bin ka’ida ya cuceka

Ka dai kammala naka

 

Bugewar barcin mai dokar gyangyadawar kotun kwance wa kasa takaddamar shari’o’i ta sanya ni cikin SALLAMIN SUKAR SAUKE SALAMI da aka taba tsuwurwurtawa a shigafar daukaka kara ta tarayyar Haorobiya. Kai hasali ma har wassafawa na yi a tunanina kan yadda Gwamnatin Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki ta wancakalar da Mai martaba Masanin Sisi-da-sisi daga jan ragamar Babban Asusun Asin Kasa. Shin wadannan al’amura an aiwatar da su ne bisa tanade-tanaden dokoki ko kuwa dukan ta-mola aka yi wa dokokin kasa, don a cimma soye-soyen zukatan masu mulkin mulaka’un Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge?

 

Ba tare da na samu amsar tambayar da na bijiro da ita ba, ina ganin hayagagar yunkurin tsige mai shari’ar da ya  yi SHIRMEN SHARRI, wajen yin kwange da kundume matsabbai wai shi ga kwage, ai ba ta kamata a bari ya sha ba. Domin in aka ci gaba da tsuwurwurta irin wannan kwakyariyar KWASHI-KWARAF ana lakume tuwo, an sha miya SHARKAF, ai sai miyagu su ji dadin tafka ta’asa.

 

Haurobiyawa kada a yi mana DAMFARAR DAMUN FURA, har ta sanya kawunanmu FURFURA ba tare da mun fasko inda aka dosa ba. Ya kamata dai kowa ya hau kurku-rido mai zuwa Gano, ko ma in ta kama a yanki tikikin tsuntsun sama don yin balaguro zuwa kasar Ghana wajen yin gane-gane. Ta’asar da babban kwabo ya tafka a kwanon tasarsa, lakabinta shi ne, “KAGEN KUNDUGE KWANGE KWAGE.

 

Bisa la’akari da irin tufka da warwarar da ake ta tafkawa, kan lamarin mai shari’ar kolin koliyo a Haurobiya, ina ganin gara a yi mai yiwuwa tun kafin lokacin ya kure. Domin kasashen duniya da dama sun tsige irin wadannan bara-gurbin da ke cutar da al’umma, koda kuwa kuskure suka yi, ballatana ma da kansa ya yi ikrarin kakaba wa kurungunsa TAGIYAR MALAM MANTAU, wai sai yanzu da aka bijiro da tabargazar da ya tafka, sai ya yi wuf ya ce, an kakaba masa TAGIYAR MALAM TUNAU.

 

Lallai mu ja na-zomon kafafen yada kwakwazo da akwakun wulkitawar hotuna da baje batutuwan kasa, su daina iza wuta. Abin da kawai ya kamata mai mukamin duk da ya san cewa ya yi aika-aika, musamman yi wa DOKA KARAN-TSAYE, to wajibi ne ya sauka daga mukami ba tare da an yi wani ka-ce-na-ce ba. Kuma duk inda aka samu managartan hujjojin da suka wanke wanda duk ake tuhuma da aikata laifuffuka, a iya SOLLE SHI/TA SOL DA SABULUN SALO a dawo da shi/ta kan mukaminsa/mukaminta. Idan kuwa aka samu akasin haka, wato mai laifi ya yi DUMU-DUMUN DAMA-DAMAR DAMAWA, sai kawai a damke shi/ta, a yi masa/mata kamun kazar kuku ko daurin goro goriya a huhu.

 

’Yan makaranta ina fatan mun fasko UNGON-GOGE mai BURGAMIN-BUGE, wanda ya yi wa doka karan-tsaye, lokacin da ya yi wa Malam Mantau fintinkau, bayan da Malam Tunau ya sha gabansa, sai ya zo daga bisani yana cewa, “ashe-ashe AU-AU!”

 

Haurobiyawa mu yi karatun ta-nastu, tare da kauce wa al’amuran da ka iya haifar wa kasa mutsu-mutsu, har ta kai ga gama-garin mutane su yi ta tsuwwa tsu-tsu tamkar za su tashi sama kamar tsuntsu.