✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanin Media Trust ya kai ta’aziyyar rasuwar Bala Wunti

Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam Bala Wunti daya daga cikin wadanda…

Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam Bala Wunti daya daga cikin wadanda suka fara tallar jaridar Daily Trust a Najeriya wanda ya rasu kwanan baya a Bauchi.

Shugaban Sashen Kasuwanci na Kamfanin Malam Yusuf Jidda ne ya jagoranci zuwa ta’aziyyar a madadin kamfanin.

Malam Jidda ya shaida wa iyalan marigayin cewa Shugaban Kamfanin Malam Kabiru Yusuf da Babban Edita kuma Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Malam Mannir Dan Ali da sauran ma’ikata suna mika ta’aziyyarsu ga ’yan uwa da iyalan marigayin kuma suna rokon Allah Ya jikansa Ya gafarta masa.

Sai ya bayyana marigayin da cewa mutumin kirki ne, haziki mai aiki tukuru wanda ya taimaka wajen sayar da jaridun kamfanin a Najeriya.

An kuma yi addu’o’i na musamman don nema Allah Ya jikan marigayin Ya gafarta masa kura-kuransa, sannan Malam Jidda ya mika kayayyakin abinci da suka hada da shinkafa da wake da taliya da samobita da sauransu ga iyalan marigayin.

Da yake mayar da jawabi, dan marigayin Hamza Bala da mahaifiyarsu sun gode wa Kamfanin Media Trust, sannan suka yi  addu’ar Allah Ya saka musu da alheri kan karamcin da aka yi musu.