Search
Subscribe
Kamfanin Shinkafa na Zangon Kangiwa zai samar da aiki ga mutum 5000

Wani injin casar shinkafa a birnin Delhi na kasar Indiya

Kamfanin Shinkafa na Zangon Kangiwa zai samar da aiki ga mutum 5000

Shugaban  Kamfanin Casar Shinkafa na Zangon Kangiwa, Dokta Hussaini Suleiman Kangiwa, ya ce kimanin mutum dubu biyar ne za su samu aiki a kamfanin da yake ginawa a Karamar Hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi.

Dokta Hussaini Kangiwa ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar duba ayyukan da injiniyoyi daga wani  kamfanin kasar China za su gudanar a wurin gina kamfanin nasa.

Ya ce: “Ma’aikata 1,500 ne za su kasance ma’aikata na dindindin, sauran 3,500 za su kasance ma’aikatan wucin gadi da na kwantaragi da kuma wadanda za ana biya a kullum.”

Ya kara da cewa, “Na yi tunanin kafa kamfanin casar shinkafa a garin Argungu ne  don samar da ayyukan yi ga jama’armu da kuma taimaka wa gwamnatin jihar da kuma ta tarayya wurin samar da aikin yi ga jama’ar kasar nan; musamman matasa da ke zaman kashe wando.

“Za mu bada tallafi ga manoman shinkafa, mu kara musu karfin gwiwar yin noma a Jihar Kebbi; musamman noman shinkafa. Tallafin zai kunshi samar musu da taki da irin shinkafa da kuma sauran kayan gudanar da aikin gona da idan sun kammala noman sai kamfani ya saye shinkafar da suka noma kamar yadda ake sayar da ita a kasuwa,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa za su kara tallafa wa manoman tare da ba su horo na zamani kan aikin noman shinkafa na zamani don kara inganta noman shinkafa a sauran kananan hukumomin jihar.

Ya ce: “Nan bada jimawa ba za mu kafa kamfanin samar da takin zamani a garin Kangiwa da ke Karamar Hukumar Arewa don samar da saukin samun taki ga manoman Jihar Kebbi, kuma nan da wata tara masu zuwa za a yi hakan.”

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin