✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Abubuwa 5 da za su dauki hankali a bana

Kamar yadda aka sani, Masana’antar Kannywood masana’anta ce da ta ba dimbin mutane aikin yi, musamman a Arewa kamar yadda takwararta ta Nollywood ta ba…

Kamar yadda aka sani, Masana’antar Kannywood masana’anta ce da ta ba dimbin mutane aikin yi, musamman a Arewa kamar yadda takwararta ta Nollywood ta ba mutanen Kudu.

A shekaru kadan da suka wuce, masa’antar ta shiga mawuyacin hali, inda har wadansu suka fara tunanin za ta durkushe, musamman kasancewar kasuwancin masana’antar ya tabarbare. Tabarbarewar kasuwancin ya sa da yawa daga cikin masu shirya fina-finai suka labe, suka yi shiru kamar ba sa nan. Wadansu suka koma wata sana’ar, wadansu kuma suka hada da wata sana’ar. Da dama daga cikin masu shirya fim suna da fina-finai ada tsoron hasara ya sa suka ajiye fina-finan ba su fitar ba. Don haka ne Aminiya ta rairayo wasu abubuwa da za su dauki hankali a masana’antar Kannywood a bana:

 

Nafisa Abdullahi za ta zama darakta

Jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa a shafinta na Instagram watannin baya cewa za ta zama darakta a karon farko.

Bayan ta shirya fim din Yaki A Soyayya, wanda ta shirya a kan matsalar shaye-shaye, kuma fim din ya yi suna sosai, kuma ya samu karbuwa matuka.

Sai likkafarta ta ci gaba, inda ta nuna cewa za ta zama darakta a karon farko a fim dinta mai suna Zainab Ali.

Nafisa Abdullahi ta wallafa cewa: “Ina bukatar addu’o’inku. Zan zama daraktar fim a karon farko.”

Tuni mutane suka rika taya ta murna da yi mata fatar alheri, ciki da har Ali Nuhu da mai shirya fim, din Naziru Danhajiya.

Jim kadan bayan ta yi wannan rubutu, sai ta cilla kasar waje domin karo karatu. Amma yanzu ta dawo bayan tsawon lokaci.

Yanzu kallo ya koma wajen Nafisa Abdullahi domin ganin yadda za ta kaya wajen bada umarnin fim din nata mai suna Zainab Ali wanda yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa.

Bashir Maishadda da Jammaje za su shirya fim ‘mafi girma’ a Kannywood

Wani furodusa da komai wuya bai tsoron kashe kudi wajen shirya fim a Kannywood shi ne Abubakar Bashir Maishadda. Duk da cewa kasuwancin fim ya yi kasa, Maishadda ya shirya fina-finai da dama a bara, kamar su Hauwa Kulu da Mariya da sauransu.

Abubakar Bashir Maishadda ya bayyana cewa shi da furodusa Kabiru Jammaje za su shirya fim mafi girma a tarihin Kannywood.

Bai bayyana yadda fim din zai zama mafi girma ba, ko kuma me ya sa zai fi girman ba. Sai dai ya bayyana cewa za su hada manyan jaruman Nollywood da manyan jaruman Kannywood a fim din mai suna The Right Choice. Sannan ya ce fim din zai ci miliyoyin Naira.

Za a fara daukar fim din ne a wannan watan na Janairu.

Tun farko furodusan ya bayyana cewa duk fina-finan da ya shirya da kuma nasarorin da ya samu kamar sharar fage ya yi.

Daga cikin jaruman fim din akwai Sani Mu’azu da Segun Arinze da Sola Sobowale da Nancy E.Isime da Enyinna Nwigwe da Ali Nuhu da Abba El-Mustapha da sauransu kuma Ali Nuhu ne daraktan fim din.

Adam A. Zango a Legas

Wani abin da masu kallo za su sanya ido su gani shi ne kasancewar jarumi kuma mawaki Adam A. Zango a Jihar Legas.

Kwanakin baya ne ya bayyana a wata hira da ya yi da Aminiya cewa zai koma Kudu da harkokinsa, inda ya ce zai fi mayar da hankalinsa kan wakoki, amma zai rika yin fim jefi-jefi, musamman in an bukaci ya yi.

Daga cikin abubuwan da zai fi mayar da hankali shi ne hadakar wakoki da mawakan Kudu, inda salon wakokin da yake yi suka fi tashe da samar da kudi.

A bara ne Zango ya bayyana cewa ya fice daga Masana’antar Kannywood, inda ya bayyana rashin adalci a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka sa ya fice daga masana’antar.

Masu kallo yanzu suna jira su ga yadda za ta kaya, ko Zango zai samu karbuwa a can Kudu, ko kuma zai dawo Arewa.

Farfado da Kadawood

Wani abin da kuma masu kallo za su zura ido su jira shi ne shirin farfado da Kadawood, wanda jaruman fim na Jihar Kaduna ke kokarin farfado da ita.

Bangaren Kadawood ya dade yana shirya fim, sai dai abin bai samu karbuwa yadda ya kamata ba, inda wadansu ke cewa bai kamata a ce akwai Kannywood ba, sannan a samu Kadawood duk a Arewa ba. Sannan wadansu sun ce kasancewar Kannywood ta riga ta yi karfi, zai yi wuya Kadawood ta daga har ta yi wani abin a-zo-a-gani.

Amma su ’yan Kadawood suna ci gaba da kokari don ganin hakarsu ta cimma ruwa.

Akwai tsofaffin jarumai a Kadawood da kamfanonin shirya fina-finai da dama, kuma suna shirya fim da dama.

Akwai Kamfanin Sabuwa Concept Nigeria Limited na jarumi kuma mawaki MD Anas da White Birds Mobies na Nura MC, wanda shi ne Shugaban Riko na Kadawood da Kamfanin Abu Namu na Isma’il Koli da sauransu.

Farfado da kasuwancin fim

Wannan burin duk wani mai ruwa-da-tsaki ne a Masana’antar Kannywood saboda tabarbarewar kasuwancin masana’antar ya shafi mutane da dama.

An yi tarurruka da dama, an kafa kwamitoci duk da zimmar ganin an shawo kan lamarin, amma abin ya ci tura.

Wadansu daga cikin masu ruwa- da-tsaki a masana’antar sun ce sun shiga siyasa ce domin tunanin idan aka samu nasara za a taimaka musu wajen farfado da masana’antarsu.

A bana, za a zuba ido a gani ko hakarsu za ta cimma ruwa.