✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillar ta kara daga martabar Arewa – Alhaji Salisu Yaro

Alhaji Salisu Yaro shi ne Jami’in Kula da Jin Dadin ’Yan Wasan Kano Pillars. A hirarsa da Aminiya ya nuna jin dadinsa game da lashe…

Alhaji Salisu Yaro shi ne Jami’in Kula da Jin Dadin ’Yan Wasan Kano Pillars. A hirarsa da Aminiya ya nuna jin dadinsa game da lashe Kofin Kalubale na Kasa (Aiteo Cup) da suka yi a karon farko cikin shekara 66.  Sannan ya bayyana  shirye-shiryensu na tunkarar Gasar Kofin Kalubale na Afirka:

Me za ka ce game da nasarar da kulob din Kano Pillars ya samu na lashe Kofin Kalubale na Kasa da ake kira AITEO CUP bayan shekara 66?

A gaskiya ba zan iya misalta murnata ba, domin abu ne da shekara da shekaru muke ta fatar samu amma sai a bana mafarkinmu ya zamo gaskiya. To ka ga babu abin da za mu yi sai godiya ga Allah da kuma dimbin magoya bayan wannan kungiya yara da manya kai har da matan aure da suke ta yi mana addu’a a kullum.

To wane kira za ka yi wa gwamnatin Jihar Kano wajen saka wa ’yan kwallon Pillars da alheri?

A’a babu wani kira da zan yi, ai ba sai mun fada mata abin da ya kamata ta yi ba. Domin ko ba komai Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Nasiru Gawuna jigo ne a kungiyar, duk abin da ya shafe ta tun can baya yana bakin kokarinsa wajen tallafa wa kungiyar ballantana yanzu da ta samu wannan nasara.  Sannan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar zai saka wa ’yan kwallon da jami’ansu da alheri kuma ya yi alkawarin karrama su da zarar sun koma Kano daga garin Kaduna.  Yanzu dai mun zuba ido ne mu ga irin goma-ta-arzikin da gwamnatin Kano za ta yi musu.

Wadanne shirye-shirye kuke yi don tunkarar wasannin da kuke daf da farawa na Kofin Kalubale na Afirka?

Tuni muka shiga horar da ’yan wasanmu inda yanzu haka suke zaune a Kaduna an killace su suna samun horo. Hakan zai ba ’yan wasan damar ci gaba da gane junansu da kuma samun kwarewa.

Ko kun sayi wadansu sababbin ’yan wasa zuwa yanzu?

Kwarai kuwa, domin tuni Gwamnatin Jihar Kano ta amince mana mu sayi duk ’yan wasan da suka kamata. Kawo yanzu mun sayo sababbin ’yan wasa bakwai sannan muna sa ran sake sayo wadansu nan gaba.

A karshe wane kira za ka yi ga magoya bayan wannan kungiya?

Ina kiran magoya bayan wannan kungiya su ci gaba da goya wa Kano Pillars baya kamar yadda suka saba ta yin addu’o’i don ganin mu samu nasarori a wannan wasa na cin Kofin Kalubale na Nahiyar Afirka da za mu fara nan da wasu ’yan kwanaki.  Bayan mun daga martabar yankin Arewa a lashe Kofin Aiteo yanzu burinmu shi ne lashe Kofin Kalubale na Afirka.