✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karancin tumaturi ne ya kawo tsadarsa a kasuwa – Aminu Yahaya

Shugaban Kasuwar ’Yan Tumatir da ke Farar Gada a garin Jos fadar Jihar Filato, Alhaji Aminu Yahaya Inusa ya ce karancin tumatir ne da ake…

Shugaban Kasuwar ’Yan Tumatir da ke Farar Gada a garin Jos fadar Jihar Filato, Alhaji Aminu Yahaya Inusa ya ce karancin tumatir ne da ake fuskanta a bana ya kawo tsadarsa. Shugaban kasuwar ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, a garin Jos.

Ya ce, kamar a nan Jihar Filato bana manoman tumatir  sun noma tumatir  amma Allah Ya sa an samu matsalolin kankara da wasu cututtuka da suka kashe tumatirin. Ya ce, wannan ne ya sa tumatirin bai wadata ba har zuwa wannan lokaci, don haka aka samu karancinsa shi ne ya sa yake tsada.

Ya ce, abin da ya shafi jihohin Gombe da Kano da Kaduna can ma an samu irin wannan matsala, don haka yanzu tumatir yake  tsada a ko’ina.

Alhaji Yahaya, ya bukaci jama’a su rungumi harkokin kasuwancin sayar da tumatir a kasar nan. “Don ci gaba da yin harkokin kananan kasuwanci, babu kasuwancin da za ka yi yanzu-yanzu ka samu abin da za ka ci riba kamar kasuwancin tumatir,’ inji shi. Ya ce, don haka yanzu da matan aure da zawarawa da sauran matasa suka rungumi harkar sayar da tumatir.

Ya yi kira ga gwamnati ta rika bai wa bangaren noma kaso mafi tsoka a kasafin kudin Najeriya, domin yanzu manoma ne suke rike da Najeriyar.