✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Keshi ya gayyaci ’yan kwallo 25

A ranar Talatar da ta wuce ne Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya fitar da jerin sunayen ’yan kwallo guda 25…

A ranar Talatar da ta wuce ne Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Stephen Keshi ya fitar da jerin sunayen ’yan kwallo guda 25 da ake sa ran zaftare bakwai su koma 18 kafin a kara da Habasha a ranar 16 ga Nuwamban nan a wasa zagaye na biyu na gasar neman hayewa zuwa cin kofin duniya da za a yi a Brazil a badi idan Allah Ya kaimu. Za a yi wasan ne a garin Kalaba.

A wannan karo kocin ya gayyato dan kwallon baya a kulob din Chelsea Keneth Omerou da kuma Reuben Gabriel da ke wasa a Sukotlan (Scotland).
Shi dai Omerou ya buga wasannin da Super Eagles ta yi guda shida a gasar cin kofin Afirka a watan Janairu amma ya ji ciwo a kafada a watan Yuni a gasar cin kofin Nahiyoyi da aka yi a Brazil watau Confederations Cup.
A wasan farko da Najeriya ta yi da Habasha, ta lallasa Habasa da ci 2-1.
Ga jerin sunayen ’yan kwallon da kocin ya kira kamar haka: Gololi (Masu tsaron gida) sun hada da bincent Enyeama (Lille FC, Faransa) da Austin Ejide (Hapoel Be’er Sheba, Isra’ila) da kuma Chigozie Agbim (Enugu Rangers). Masu tsaron baya (Defenders): Elderson Echiejile (Sporting Braga, Portugal) da Francis Benjamin (Heartland, Owerri) da Efe Ambrose (Celtic, Scotland), da Solomon Kwambe (Sunshine Stars, Ibadan) da Godfrey Oboabona (Rizerspor, Turkiyya) da Azubuike Egwuekwe (Warri Wolbes) da James Okwuosa (Chippa United, Afirka ta Kudu) da kuma Kenneth Omerou (Chelsea, Ingila). Masu tsaron tsakiya (Midfielders) an kira: John Mikel Obi (Chelsea, Ingila) da John Ogu (Academica de Coimbra, Fotugal) da Ogenyi Onazi (SS Lazio, Italiya) da Nosa Igiebor (Real Betis, Sifen) da bictor Moses (Liberpool, Ingila) da Sunday Mba (Enugu Rangers) da Nnamdi Oduamadi (Brescia, Italiya) da kuma Rueben Gabriel (Kilmarnock, Sukotlan). Masu wasa a gaba kuma an kira: Ahmed Musa (CSKA Mosko) da Brown Ideye (Dynamo Kyib, Ukraine) da Shola Ahmed (Newcastle United, Ingila da Emmanuel Emenike (Fenerbahce, Turkiyya), da Obinna Nsofor (Lokomotib Moscow, Rasha) da kuma Uche Nwofor (SC Heerenbeen, Netherlands).