✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kirkiro Masarautu: Ganduje ya sake aika wa majalisa sabon kuduri

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar dokokin jihar, domin kafa sabbin masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye.…

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar dokokin jihar, domin kafa sabbin masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, ya fitar da sanarwar a yau Litinin, wanda a yanzu haka majalisar ta karbi sabon kudurin a zauran majalisar.

Majalisar zartarwa ta sake aika wa da sabon kudirin ne wanda da zai iya bayar da damar kafa sabbin masarautun hudu.

Kwanaki kadan kenan da wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce, ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka’ida ba.