✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kobe Bryant da ‘yarsa sun mutu a hadarin jirgin sama

Fitaccen dan wasan kwallon kwando Ba’amurke Kobe Bryant na daga cikin mutane tara da jirgin helokofta da suke ciki ya yi hadari a birnin Calabasas…

Fitaccen dan wasan kwallon kwando Ba’amurke Kobe Bryant na daga cikin mutane tara da jirgin helokofta da suke ciki ya yi hadari a birnin Calabasas na California, a jiya Lahadi.

Kobe Bryant, mai shekara 41 da ‘yarsa mai suna Gianna mai shekara 13 sun mutu ne bayan da jirgin sama mai saukar angulu da suke cike ya fado sannan ya kama da wuta.

Ana yi wa dan wasan kwallon kwando da ya ke rike da kambu biyar na Kwallon Kwando NBA kallon gawurtacce a duniyar wasan kwallon kwando ba za ta taba mantawa da shi ba a tarihi.