✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Koriya ta Arewa na bata yarjejeniyar mallakar makaman nukiliya’

Jakadan Amurka na musamman a Koriya ta Arewa ya kai ziyara birnin Pyongyang domin tsara yadda taron koli na biyu a tsakanin Shugaba Donald Trump…

Jakadan Amurka na musamman a Koriya ta Arewa ya kai ziyara birnin Pyongyang domin tsara yadda taron koli na biyu a tsakanin Shugaba Donald Trump da takwaransa Kim Jong-un zai kasance.

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan wani rahoto da Majaisar Dinkin Duniya ta fitar da ke cewa Koriya ta Arewa na ci gaba da yi wa takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba mata karan-tsaye, takunkumin da aka saka domin hana ta mallakar makaman nukiliya.

Rahoton ya ce Koriya ta Arewar tana shigar da kayayyakin da take bukata cikin kasar ta haramtacciyar hanya, matakin da ke nufin takunkumin na Majalisar Dinkin Duniya ba ya aiki ke nan.

Shugaba Donald Trump ya yaba wa Koriya ta Arewa domin gagarumin ci gaban da ta samu wajen kwance damarar samar da makaman nukuiliya.

Wadannan kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da yake shirin ganawa da Kim Jong-un cikin makonni masu zuwa.

Amma rahoton Majalisar Dinkin Duniya na cewa shirin mallakar makaman nukiliya na Koriya ta Arewar na ci gaba da bunkasa kamar yadda BBC ya ruwaito.

Wani abin da zai damu  Trump shi ne rahoton ya bayyana cewa takunkumin karya tattalin arziki da Amurka ta kakaba wa kasar domin matsa mata ta sauya alkibla bai yi tasiri ba.

Jami’ai masu sa ido sun gano cewa an samu karuwa sosai na makamashi kamar mai da kwal ta hanyar amfani da jiragen ruwa da kan saci hanya domin batar da kama.

Sun kuma yi ikirarin suna da hujjar da ta nuna an shigar da makamashi na kusan Dala miliyan shida cikin kasar.

Rahoton ya kuma zargi Koriya ta Arewa da taka wasu dokokin majalisar da suka hana ta sayen makamai da sayar da makamai ga kungiyoyi masu dauke da makamai da wasu gwamnatoci a Gabas ta Tsakiya da Nahiyar Afirka.