Da Dumi Dumi

Kotun Koli ta saki Sanata Orji Uzor Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu

Kotun Kolin Najeriya ta soke hukuncin daurin da aka yanke wa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Ozor Kalu, bayan da aka same shi da laifin almundahana ta sama da Naira biliyan bakwai.

Wadanda aka yanke wa Kalu hukuncin tare da su, wato kamfaninsa, Slok Nigeria Limited, da tsohon kwamishinansa na kudi, Ude Jones, su ne suka daukaka kara suna kalubalantar hurumin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke hukuncin.

Sun kafa hujja ne da cewa a lokacin da alkalin Babbar Kotun, Mai Shari’a Mohammed Liman, ya yanke hukuncin, an yi masa karin girma zuwa Kotun Daukaka Kara, amma ya dawo don ya karasa shari’ar.

Da yake karanta hukuncin Kotun Kolin ranar Juma’a, Mai Shari’a Ejembi Eko ya ce yadda aka yi amfani da sashe na 396(7) na Dokar Hukunta Manyan Laifuffuka ta 2015 ya saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Da yake maida martani Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce ya sadaukar da rayuwarsa ga duk ’yan Najeriya wajen ci gaba da kalubalantar shari’ar da ake yi masa.

ADVERTISEMENT

Tsohon gwamnan Abiya ya bayyana hakan ne ranar Juma’a lokacin da yake amsa tambayoyi game da hukuncin kotun koli na yanke masa hukuncin zaman kaso na shekara 12, inda ya ki amincewa da umarnin kotun.

A wani jawabi da Kalu ya rattaba wa hannu, ya ce kotun bata ba shi damar kare kansa ba, da kuma ’yancin da doka ta tanadar ba.

Ya kara da cewa, a zamansa a gidan gyara halinka na tsawan wata biyar, ya koyi wasu darussa game da tsarin shari’ar Najeriya da kuma ma’anar kauna ta gaskiya.

A cewar Kalu, “Zaman  wata biyar da nayi ya ba ni damar sanin batutuwan shari’a da kuma tauye hakkin shari’ar Najeriya da ake yi. Na kai matsayin sanin muhimmancin shari’ar da ake yi min, kuma ba zan san muhimmanci shari’a ba idan na janye tuhumar da ake yi min.” Zan ci gaba da kalubalantar hukuncin har sai shari’ar ta taba zukatan miliyoyin ’yan Najeriya da ake tauye hakkinsu a duk inda suke a duniya.

“Zan sadaukar da lokacina nan gaba don tabbatar an yi wa duk ’yan Najeriya adalci koda wadanda suke jihohin Sakkwato ne ko Akwa Ibom ko Legas, ko Maiduguri ko wadanda suke Jos ko Enugu koma duk inda suka fito.

Sashen dokar ne dai Shugabar Kotun Daukaka Kara ta lokacin, Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, ta dogara da shi ta bai wa Mai Shari’a Liman damar zuwa ya kammala shari’ar,

Don haka ne Kotun Kolin ta ba da umarnin a sake shari’ar.

Ranar 5 ga watan Disamban bara ne dai aka yanke wa Orji Uzor Kalu, wanda a yanzu dan majalisar dattawa ne, hukuncin zaman kaso na shekara 12; kuma yanzu haka yana garkame a gidan yari na Ikoyi.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya