Da Dumi Dumi

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Aliyu

Babbar kotun koli ta tabbatar da  Suleiman Aliyu Lere a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Lere, a Jihar Kaduna, a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan fabreru,2019.

Kotun mai alkalai 5 ta zartar da wannan hukunci ne a ranar jumma’a, inda ta bayayyana cewar, shigar da karar ma da aka yi bata da wani tushe, domin haka aka yi watsi da ita.

Da yake zartar da hukunci Mai shari’a Bode Rhodes-Bibour, wanda Mai shari’a Uwani Abba-Aji ta karanto, cewa tayi babbar kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta Kaduna ta zartar akan takaddamar. Kotun dai a ranar 11 ga watan afrilu, tayi watsi da karar da Ahmed Munir ya shigar, wanda ya shiga neman takarar jamiya ta bashi damar tsayawa neman wannan kujera, a takarar da aka fitar da Lere a matsayin dan takarar kujerar majalisar wakilai a jamiyar APC, da aka yi a watan oktoba, 2018, Sai dai kawai Jamiyar ta sai tura sunan Munir ga hukumar zabe a matsayin shine dan takarar kujera majalisar wakilai.Ba tare da bada wani dalili na yin hakan ba, Hakan tasa matakin da jamiyar APC ta dauka bai yi wa Suleiman Aliyu dadi ba, wanda shine tsohon kwamishinan albarkatun ruwa a jihar kaduna, inda ya kalubalanci  hukunci da jamiyar ta dauka,na sauya sunan sa, hakan tasa ya garzaya zuwa babbar kotun dake jihar ya shigar da kararsa, sai dai kotun ta yi watsi da karar ta sa, domin tace bata da hurumin saurarar karar.Tsohon kwamishinan sai ya sake shigar da kokensa akan abin da kotun tayi,sai dai kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa shi, Suleiman Aliyu, shine sahihin dan takarar kujerar.

Amma sai Munir ya ki gamsuwa da wannan hukunci da kotun daukaka karar ta zartar inda ya kai lamarin gaban Kotun Koli, har ta yanke wannan hukunci na tabbatar wa Suleiman Aliyu kujerar.

ADVERTISEMENT
Share