✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuikwiyo mai kunne daya a tsakiyar goshi ya samu karbuwa

Wani kuikwiyo da aka haifa ya rasa kunnensa daya bayan karyar da ta haife shi ta gantsara masa cizo a kunnen bangaren hagu kwana biyu…

Wani kuikwiyo da aka haifa ya rasa kunnensa daya bayan karyar da ta haife shi ta gantsara masa cizo a kunnen bangaren hagu kwana biyu da haihuwa, hakan ya sa kunnensa na dama ya koma tsakiyar goshinsa bayan an yi masa tiyatar raunin da ya samu.

Akwai masoya kuikwiyo masu sha’awar irin wadannan karnuka da yawa a kafafan sada zumunta musamman na Instagram inda hakan yake nufin cewa, zai yi wahalar gaske a rasa mai son kuikwiyon wanda ya kasance na musamman. Duk Kuikwiyon da ake kira da “Golden Unicorn” yana daukar hankalin jama’a saboda siffarsa.

Hadarin da ya faru da shi jim kadan da haihuwarsa ya sanya sunansa ya yadu a shafukan sadarwa musamman TikTok, inda wani hoton bidiyo ya nuna kuikwiyon da wata siffa ta musamman kuma mai ban mamaki.

Hoton bidiyon ya samu karbuwa a wurin sama da mutum dubu 500 a shafukan sada zumunta, bayan an dora hoton bidiyon na biyu wanda ya nuna yadda kuikwiyon ke wasa.

Bayan tambayar wani likitan dabbobi wanda ya sanya hoton bidiyon ya bayyana cewa, “Mahaifiyarsa ce ta cije masa kunne kwana biyu da haihuwarsa. Hakan ya sa ya rasa kunnen kuma sai dayan ya koma tsakiyar goshinsa.”

Likitocin dabbobi sun ce, kuikwiyon wanda wadansu suka bayyana a matsayin abu mafi kyau da suka taba gani, yana iya ji da kunnen.

Shafin Instagram da aka bude saboda tura hotuna da bidiyon kuikwiyon ya samu mabiya sama da dubu 12, yayin da yake ci gaba da samun karbuwa.

Wannan kuikwiyon yana da doguwar jela da kunne daya a tsakiyar goshi, kuma an ceto shi ne a wani yanki da ke kusa da kasar Kanada da wani yankin kasar Rasha da suke da yanayin sanyi.

Wadansu ma’aikatan ceto dabbobin daji na Mac’s Mission, sun rada wa kuikwiyon suna Narwhal, nan take shafin kuikwiyon ya samu karbuwa matuka bayan wallafa bidiyon a shafin sada zumunta na Facebook

Ma’aikatan sun bada gagarumar gudunmawa wajen kula da kuikwiyon da aka yi watsi da shi saboda sauyin halittarsa bayan samun raunin.