Kungiyar Intansurullah ta shirya bita a Kafanchan

‘Ya’yan Kungiyar Intansurullah bayan kammala taron bita
‘Ya’yan Kungiyar Intansurullah bayan kammala taron bita

Kungiyar Intansurullah Yansurkum da ke garin Kafanchan a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, ta shirya taron bita na wuni daya don fadakar da mata da matasa illolin shaye-shaye ga rayuwar matasa da kuma muhimmancin taimako a Musulunci.

Da yake gabatar da jawabi na farko kan muhimmancin taimako, Malam Baba Tanko, ya ce addinin Musulunci ya koyar da taimaka wa duk mai bukatar taimako ba tare da la’akari da addininsa ba, ballantana akidarsa ko inda ya fito.

Malamin, wanda ya yi kira ga mutane cewa kowa ya duba ya ga irin gudunmawar da zai iya bayarwa a cikin al’ummar da yake zaune a ciki, ya ce babban matsalar da ta jefa al’ummar kasar nan a cikin halin ni-’yasu ita ce rashin taimako.

“Babu wani mai taimako da ya wuce Allah; amma kuma duk da haka Shi Ya umarce mu kan mu zamo masu taimakon juna domin Ya yi amfani da wannan dama wajen yaye mana mummunan halin da muke ciki,” inji shi.

Sannan ya bayyana hanyoyin taimako daban-daban da mutum zai iya bayarwa a cikin al’umma ba lallai sai ya kasance na kudi ba.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake gabatar da nasa jawabi kan illolin shaye-shaye, Malam Yahaya Usman Rahama, ya ce abin takaici ne a ce Allah Ya karrama dan Adam da hankali wanda ya bambanta shi da dabbobi, amma ya dauki dukiyarsa ya sha abin da zai gusar masa da hankali., Ya ce hakan babban butulce wa Allah ne; wanda mummunan sakamakonsa a fili yake ga rayuwar mai aikatawa tun a duniya kafin mugun sakamakon da zai tarar a ranar Lahira.

“Baya ga asarar dukiya da bata kima da zubar da mutunci, shaye-shaye kan cutar da kwakwalwa da lafiyar jiki; sannan su jefa mutum ga aikata sauran laifuffuka inda a karshe mutum zai rasa Lahirarsa,” inji shi.

Tun farko, Shugaban Taron, Malam Ibrahim Musa, ya jinjina wa kungiyar da dukkan matasa  sannan ya yi kira ga jama’a su rika muhimmantar da lokaci a rayuwarsu.

A jawabin Shugaban Kungiyar, Muhammad Kabir Sagir, ya ce sun assasa kungiyar ce sakamakon karfafawa daga jama’a da malamai da kungiyoyi da kuma gwamnati da suke fadakarwa kan yadda wadansu za su tashi tsaye don taimaka wa jama’ar da ke kusa da su musamman marayu da marasa karfi da majinyata.

“Ni kaina na tsinci kaina a matsayin marayar da bai riski daya daga cikin iyayena ba; wanda tasirin taimakon da na samu a rayuwa ya sanya ni tunanin daukar wa kaina niyyar taimaka wa duk wanda ya tsinci kansa a irin wannan hali da na tsinci kaina,” inji shi.

Ya kara da cewa babban makasudin kafa kungiyar Intansurullah, shi ne zaburar da masu hali kan yadda za su lura da masu bukatar taimako da ke rayuwa a cikinsu da samar da kyakkyawar alaka da hadin kai a tsakanin matasan garin Kafanchan tare da taimakawa wajen aiwatar da ayyukan alheri.

“Daga cikin ayyukan da muka aiwatar a kasa da shekara biyu, akwai taimaka wa marayu  54 ta hanyar biya musu kudin makarantun addini da sakandare, inda muka biya wa marayu 13 kudin makaranta.”

Ya ce sauran ayyukan kungiyar  sun hada da taimaka wa masallatai da shimfidu da taimaka wa majinyata marasa karfi ta hanyar biya musu kudaden magani da raba kayan abinci a watan azumin Ramadan da sauransu, inda ya ce nan gaba suna da burin samar da tallafin sukolashif ga ’ya’yan marasa galihu masu kwazo.

Da yake sanya albarka a karshen taron, Magajin Garin Jama’a, Alhaji Abubakar Sadik Isa, wanda Alhaji Isyaka Abdu Ladan ya wakilta, ya bayyana farin cikinsa da samuwar irin wadannan matasan a wannan yanki, inda ya ce hakan na nuna kyakkyawar fata da makoma mai kyau ga rayuwar al’ummar masarautarsa da kuma kasa baki daya.

Share