Da Dumi Dumi

Kungiyar Matasa ta bukaci a kafa kwamitin bincike kan hare-hare a Karamar Hukumar Kaura

Kungiyar Matasan Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna ta yi kira ga gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai binciki rikice-rikice don duba harin da wadansu ’yan bindiga suka kai a garin Zangan da ke karamar hukumar da ke iyaka da Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato don zakulo maharan tare da duba hanyoyin da za a bi don magance tashe-tashen hankula a yankin.

Kiran na kunshe ne cikin wata takarda da Shugaban Kungiyar ta Kasa, Kwamared Derek Christopher ya sanya wa hannu inda ya ce hakan na daga cikin matakan da za su haifar da da mai ido a tsakanin al’ummomin kananan hukumomin biyu.

Kungiyar ta mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin, ta kuma yi kira ga gwamnati da kungiyoyin jinkai su gaggauta kai musu dauki ta hanyar samar musu da tallafin gaggawa a sansanonin ’yan gudun hijirar don rage musu radadin halin da suke ciki.

Kungiyar ta yi kira  a samar da matsugunin jami’an tsaro na dindindin tare da karo jami’an tsaro a yankin don rage yawan tashe-tashen hankulan da ke addabar yankin.

Kungiyar ta jinjina wa Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Mista Bege Ayuba Katuka, da Sarkin Attakar, Mista Nkom Wada kan matakan da suka dauka wadanda suka taimaka wajen takaita hasarar da jama’ar yankin suka yi.

ADVERTISEMENT

Yayin da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna Yakubu Sabo ya tabbatar da rasuwar mutum biyar a harin, kungiyar ta matasan Kaura ta ce mutane bakwai ne suka rasa rayukansu tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira.

Share