✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Matasan Izala ta shirya taro kan tarbiyyar yara a Nasarawa

Kungiyar Matasa ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya taron bayar da horo na yini uku ga matasa inda aka gabatar da…

Kungiyar Matasa ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta shirya taron bayar da horo na yini uku ga matasa inda aka gabatar da laccoci kan al’amuran da suka shafi tarbiyyarsu. Taron ya gudana ne a makarantar Alhidaya da ke garin Maraba a Karamar Hukumar Karu a Jihar Nassarawa a karshen makon jiya.

A jawabin da ya gabatar, Uban kungiyar na yankin Malam Yusuf Idris Farin-Ruwa, ya ja hankalin mahalarta taron ne kan illolin shan miyagun kwayoyi da kuma tasirinsa wajen haddasa fitinu ga al’umma baki daya.

Malam Yusuf Idris wanda har ila yau shi ne shugaban makarantar Alhidaya da ke Maraba, ya bukaci iyaye musamman mata wadanda ya ce sun fi kusanci da yara, su sa ido sosai wajen tarbiyyarsu tare da tabbatar da cewa ba su cudanya da miyagun ayyuka ba.

Ya ce kasancewar matasa su ne za su karbi ragamar shugabanci a lokacin da jagorori na yanzu ke bukatar magada, akwai bukatar a rika jansu a jiki tare da sanya su a kan al’amura a matsayin horo.

Shugaban Kungiyar Matasan Kungiyar ta Jihar, Ustaz Shu’aibu Wamba ya gargadi matasan su guji ba da kansu wajen ayyukan daba musamman a lokacin siyasa, sannan ya hore su da su rungumi karatun addini da na boko don zama masu amfani ga kansu da kuma al’umma baki daya.

Da yake bayani a kan nasarorin da kungiyar ta samu, Mataimakin Shugaban Kungiyar, Malam Abubakar Ibrahim ya ce a lokacin da kungiyar ta faro kamar shekara biyu da suka wuce ta fara ne da mambobi biyar, amma a yau tana da matasa mambobi fiye da dubu biyar.

Sai dai ya ce a yanzu kungiyar na da mambobi kamar 60 da suka hada da bangaren maza da mata da ke kai ziyara zuwa wuraren da ake bukatar fadakarwa kamar gidajen kurkuku da aisbitoci da kuma makarantun boko. Ya ce kimanin mutum 600 ne suka halarci taron da kungiyar ta shiya na wannan karo.

Sauran malaman da suka gabatar da jawabi a yayin taron sun hada da Malam Ibrahim Attauhidi da Malam Yusuf Musa Zariya da Malam Mubarak Alfullati sai kuma Malam Ibrahim Yunusa Ibn Hazam. Haka kuma taron ya samu halartar matasa maza da mata da kuma iyaye mata.