Da Dumi Dumi

Kungiyar ZEDA za ta yi gangami kan yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi

A yau ne Kungiyar Zaria Education Debelopmeny Association (ZEDA) za ta yi wani gangami kan yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi a Kwalejin Barewa da ke Zariya.

Shugaban Kungiyar, Dokta Alimi Bello ne ya sanar da haka lokacin da ya jagoranci ayarin shugabannin kungiyar zuwa babban ofishin Media Trust da ke Abuja.

A cewarsa, “Kwana biyu za mu yi. Ranar farko za mu yi taro ne, inda za a gudanar da lacca a kan tu’ammali da miyagun kwayoyi wanda Farfesa Ahmed Tijjani Mora zai gabatar,” inda ya kara da cewa tsohon Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Alhaji Umaru Dembo ne zai zama shugaban taron.

Dokta Alimi ya ce taron zai tattauna a kan matsalolin tu’ammali da miyagun kwayoyi a Arewacin Najeriya, abubuwan da suke jawo su, da hanyoyin magance su.

“Gobe ne za mu yi babban taronmu na shekara-shekara wato AGM. A wannan taron wanda tsohuwar Shugabar Alkalan Jihar Kaduna Mai shari’a Rahila Hadea Cudjoe za ta shugabanta, Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalaong ne zai zama babban bako na musamman, sannan Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ne mai masaukin baki. Sai Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya zama uban taro,” inji shi.

ADVERTISEMENT

 

 

Share