Daily Trust Aminiya - Kurona na illa ga kudin shigar Najeriya – Buhari
Subscribe

Shugaba Muhammadu Buhari dan asalin jihar Katsina ne

Kurona na illa ga kudin shigar Najeriya – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce barkewar cutar Kurona na illa ga babbar hanyar samun kudaden shiga na Najeriya. Shugaba Buhari yana magana ce a kan illar da cutar ke yi kai-tsaye kan kudin shigar kasar nan yayin da yake karbar ma’aikatan lafiya karkashin Kungiyar Kananan Ma’aikatan Kiwon Lafiya ta Kasa (JOHESU) da kuma Kungiyoyin Kwararrun Ma’aikatan Kiwon Lafiya (AHPA) a fadarsa a Abuja.

Ko a ranar Litinin, Gwamnatin Tarayya ta sanar da yiwuwar duba batun rage kasafin kudin kasar nan na bana na Naira tirilayan 10.6, sakamakon yadda barkewar cutar Kurona ke shafar farashin man fetur a kasuwar mai ta duniya.

Shugaba Buhari yayin da yake yi wa mambobin kungiyoyin JOHESU da AHPA bayani, ya yi kira ga ma’aikatan lafiya su kara yin hakuri da gwamnatinsa game da bukatunsu yayin da gwamnatin ke kokarin tunkarar kalubalen da cutar Kuronan ke haifar wa ga tattalin arzikin kasa.

Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tana la’akari da matsalolin nasu da nufin gano bakin zaren.

“Lallai ana lura da batutuwan naku; sai dai dole ne kuma ku yi la’akari da halin da kasar ta tsinci kanta a ciki a halin yanzu. Cutar Kurona tana kawo mana tasgaro sosai, tana shafar abin da muka fi dogara da shi, wato harkar man fetur, wanda hakan ke nufin kudaden shigarmu na raguwa,” kamar yadda Buhari ya fada a cikin wani jawabi da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar.

texem
More Stories