✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama motoci 153 da buhuhunan shinkafa sama da dubu 8

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya wato (Kwastam), ta sake kama motoci akalla 153 na buhuhunan shinkafa sama da dubu takwas a cikin watanni shida.…

Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya wato (Kwastam), ta sake kama motoci akalla 153 na buhuhunan shinkafa sama da dubu takwas a cikin watanni shida.

Kwamturolar shiyyar Zone B Sarkin-Kebbi Muhammad Mustapha, ne ya sanar da hakan a yau ga manema labarai a Kaduna.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar ta kama kwalin taliyar spaghetti 820 da buhun suga 167 da jarkan man gyada  1,035 sai tsaffin tayoyin mota 3,33 da kwalin kwayar tiramadol 1,550.

Ya shawarci ‘yan kasa da kaucewa yin fasa kwauri domin a cewarsa hukumarsu na iya kokarinta wajen kare kan iyakokin kasar nan.

Sarkin-Kebbi Muhammad Mustapha ke nunawa manema labarai buhuhunan shinkafa da suka kama

Ya kuma bayyana cewa, ‎akalla mutum 14 aka kama biyu tuni an yanke masu hukunci, uku kuma suna gaban kotu a yayin da sauran kuma suna fuskantar bincike da zarar an kammala binciken za’a gabatar da su gaban kotu.