Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

La-Liga:  Gobe za a gwabza a tsakanin Barcelona da Atletico Madrid

Barcelona da Atletico Madrid

Magoya bayan Man United sun nuna fushinsu a kan Rojo da Romero

A ranar Talatar da ta wuce ne magoya bayan kulob din Manchester United da ke Ingila suka nuna bacin ransu a kan yadda ’yan kwallon kulob din biyu Marocs Rojo da Sergio Romero suka rika yin dariya a kan benci a daidai lokacin da kulob din Wolbes yake lallasa na United da ci 2-1 a gasar firimiyar Ingila.

ADVERTISEMENT

An hango wadannan ’yan wasa biyu ne zaune a kan benchi suna murna a lokacin da kulob din Wolbes ya lallasa na United.

Hakan ya bakantawa magoya bayan United rai inda suka nemi mahukunta kulob din su sayar da ’yan wasan a karshen kakar wasa ta bana saboda yadda suka nuna rashin kishi.

ADVERTISEMENT

Wannan rashin nasara da United ta samu ya jefata a cikin matsala ganin da wuya ne ta kare a matakin kulob hudu da ke sahun farko a gasar kuma hakan zai sa ta rasa gurbi a gasar zakarun kulob na Turai a badi in dai ba ta lashe kofin a bana ba.