Da Dumi Dumi

Ladi-Mutu-Ka-Raba ta rasu

A ranar Asabar da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitacciyar jaruma Ladi Mohammed wace aka fi sani da Ladi Mutu-Ka-Raba rasuwa.

Marigayiyar ta rasu tana da shekara 53 bayan ta yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Darakta Hasasan Giggs ya bayyana marigayiyar a matsayin mai hakuri wacce ta san abin da take yi. “Na yi aiki da ita ba sau daya ba, na sha fadi cewa mace ce da ta san abin da take yi. A duk lokacin da aiki ya hada ku da ita ba ta wasa tana yin abin da gaske. A gaskiya rasuwarta gibi ne babba a wannan masana’anta da cike shi sai an yi a hankali,” inji shi.

Jaruma Asama’u Sani kawar marigayiyar ce da ta  ce, “Muna tare da ita fiye da shekara 26, mace ce mai saukin kai ba ta da matsala. Kai mu mun zarce kawaye domin mun zama ’yan uwan juna. Muna mata fatar samun rahamar Allah.”

Marigayiyar ta rasu ta bar ’ya’ya uku da jikoki 14. Tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

ADVERTISEMENT

Idan za a iya tunawa a baya lokacin da ta yi rashin lafiya wadansu sun suka rika sanya hotonta a shafukan sada zumunta suka rika nema mata taimakon kudin magani lamarin da jarumar  ta fito ta tabbatar da cewa ta yi rashin lafiya, amma ba ta nemi taimakon kowa ba,  don haka ta yi kira ga jama’a da kada su bayar da kudinsu a wancan asusun banki da aka nemi a sanya kudin taimakon.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya