Daily Trust Aminiya - LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin Tambayoyi
Subscribe

LAFIYAR MATA DA YARA – Amsoshin Tambayoyi

Da ma ciwon sankarau da sanyi ake yin sa ba da zafi ba?

Na ji ana sanarwa a kafafen watsa labarai a kai yara allurar rigakafin sankarau. Da ma ciwon sankarau da sanyi ake yin sa ba da zafi ba?

Daga Munir Sani

Amsa: Ehj a watannin bazara aka fi yin ciwon, tun daga karshen sanyi zuwa farkon zafi, a watannin Fabrairu zuwa Mayu, amma ana allurar tun yanzu ne domin a yi wa ciwon tanadi da wuri, tunda an karato lokacin da akan yi ciwon.

Idan zan yi al’ada duk wata sai na yi ciwon mara da na mama da na tafin kafafu. Ko shin hakan na nufin akwai matsala?

Daga Hajara I, Kano

Amsa: A’a in dai sai wata-wata lokacin al’ada kadai yake miki, to ba matsala, watakila canjin sinadarai na hormones ne. Amma in dai ba wajejen lokutan al’ada ba ne, to, shi ne za ki damu ki dauki mataki. Wadansu mata da yawa idan suka girma suka haihu abin na yin sauki.

Me ya sa ciwon kanjamau ya fi kashe maza fiye da mata? Domin sai in ga kamar kafin ya hallaka mace guda ya hallaka maza biyar ko 10?

Daga Mukhtar Gafai, Katsina

Amsa: A’a wannan abin da kai ka lura da shi a yankinku ke nan watakila. Amma binciken kimiyya duk mata ya dora wa wahalar wannan ciwo. Wato bincike ya tabbatar mata suka fi maza saurin kamuwa da wannan ciwo, watakila saboda halayyar dan Adam ta cewa namiji kan yi mata da yawa amma da wuya mace ta yi maza da yawa. Sa’annan an nuna cewa matan suka fi shan wahalar wannan ciwo fiye da maza, su kuma suka fi mutuwa daga ciwon har ila yau. Wannan a bincike na gaba daya ke nan, amma ba za a iya rasa dan bambanci ba nan da can, kamar yadda kai ka lura

Wai da gaske ne ciwon hanta na hepatitis ya fi kama mutane da sauri fiye da na kanjamau? Idan haka ne mene ne dalili?

Daga Mujtaba Saleh, Katsina

Amsa: Eh, kuma a’a. Wato zai iya zama haka ne saboda watakila masu dauke da ciwon hanta sun ninka masu dauke da kanjamau wajen ninki 10, domin akwai masu ciwon hanta na hepatitis kusan miliyan 350, amma masu dauke da kanjamau a duniya ba su fi miliyan 40 ba. Ke nan saboda yawan masu ciwon hanta na hepatitis ciwon zai iya fin kanjamau yaduwa, duk da cewa hanyoyin da ake kamuwa da cututtukan biyu duka kusan daya suke.

texem
More Stories