✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lokaci ya yi da za a dawo da martabar masarautunmu

A wannan zamani, daraja da martabar masarautun gargajiya na kara balbalcewa, suna kara rage kima a idanun al’umma, duk kuwa da irin dimbin muhimmancinsu ga…

A wannan zamani, daraja da martabar masarautun gargajiya na kara balbalcewa, suna kara rage kima a idanun al’umma, duk kuwa da irin dimbin muhimmancinsu ga al’umma. IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya ankara cewa bai kamata a ci gaba da tafiya a haka ba, ga yadda yake son abin ya kasance:

Tilas a yi gyara a kan shirun da Kundin Tsarin Mulkin kasar nan ya yi a kan fayyace matsayi da ayyukan sarakuna a kasar nan da kuma dokar da ta ce sarakunan gargajiya suna a karkashin karamar hukuma. Domin wannan abu ne da aka yi da gangan don kaskantar da masarautun gargajiya, musamman Sarakunan Daular Usmaniyya.

Ko a zamanance, idan ka kalli sarakunan da muke da su a yau, za ka iske mutane ne da suka taka duk wani mataki a ilimi, walau na boko ko na addini. Mafi yawansu sun kai manyan matsayi kuma sun taka duk wani mataki. Sun kuma yi mu’amala da jama’a iri-iri, sun zagaya duniya kuma babu inda za a layance musu. Da damansu sukan karbi sarautar ce a lokacin da suke rike da manyan mukamai. A haka suke yin murabus don su zo su gaji gidansu.

To in kuwa haka ne ina ganin ba a yi musu adalci ba, a mai da su a karkashin  shugabannin kananan hukumomi, wadanda idan ta yi wani juyin wadansunsu yara ne da ba su taba ko rike wani mukami ba a aikin gwamnati. Sannan watakila takardar shaidar karatun sakandare kawai suke da ita. Kai a matsayi da kima irin ta sarakunan da muke da su, bai kamata a ce ko Gwamna ko wani minista zai iya ba su umarni kai-tsaye ba, ballantana har ya taka rawa ta dora su ko kuwa uwa-uba tsige su daga kan kujera. Kowace masarauta tana da irin tsarinta na zaben wanda zai gaji sarauta bisa al’ada da cancanta. Kujerarsu ba a sayarwa a kasuwa, kuma ba hawa munbarin siyasa ake yi ba a yi ihu da shewa, sannan a fadi kalamai nan a karya da yaudara wajen nemansu. Kujeru ne na musamman da suke na dindindin da ba kowane karabiti ke iya hawa kansu ba, komai kudinsa da iliminsa da sunansa sai ya gada tukunna.

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.