✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikata na jagorantar zanga-zanga a Sudan

Jami’an tsaro a Sudan sun tsare wadansu malaman jami’a da ke zanga-zanga a Khartoum, Babban Birnin Kasar. Haka kuma likitoci da dama sun fito zanga-zanga…

Jami’an tsaro a Sudan sun tsare wadansu malaman jami’a da ke zanga-zanga a Khartoum, Babban Birnin Kasar.

Haka kuma likitoci da dama sun fito zanga-zanga a asibitoci inda suke kira ga Shugaban Kasar ya sauka daga shugabancin kasar, baya ga jama’ar kasar da tun watan Disamban bara suke karawa da jami’an tsaro.

Kungiyar Human Rights Watch mai fafutikar kare hakkin dan Adam ta ce jami’an tsaro sun kashe akalla mutum 50.

Ba kamar yadda aka saba gani a wasu sassa na Nahiyar Afirka ba, inda yawancin masu fita zanga-zangar adawa da gwamnati kan kasance matasa marasa aikin yi a Sudan likitoci maza da mata da malaman makaranta da sauran ma’aikata ne ke fuskantar harsasai da hayaki mai sa hawaye da kuma kulakan ’yan sandan gwamnatin Shugaba Omar Al-Bashir.

Mako biyu da suka gabata gwamnatin Sudan ta ce za ta saki dukan wadanda ta  kama sakamakon zanga-zangar da aka shafe fiye da wata biyu ana yi a fadin kasar. Amma yawancin wadanda ke tsaren ba su samu ’yancinsu ba kamar yadda BBC ya rawaito.