✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai shekara 107 da ya shekara 96 yana sana’ar aski

Wani tsoho mai suna Anthony Mancinelli mai shekara 107, ya shafe shekara 96 yana sana’ar  aski. Duk da tsufar da ya yi a sana’ar har…

Wani tsoho mai suna Anthony Mancinelli mai shekara 107, ya shafe shekara 96 yana sana’ar  aski. Duk da tsufar da ya yi a sana’ar har yanzu yana ci gaba da aski ba tare ya yi tunanin yin murabus daga sana’ar ba.

Anthony Mancinelli yana da shagon aski a Unguwar New Windsor, da ke Jihar New York a Amurka, wannan tsoho mai aski ya fara ne tun yana da shekara 11 bayan ajiye karatunsa don dogaro da sana’ar aski.

A lokacin da ya cika shekara 96 yana aski ya shiga Kundin Tarihi na Duniya ‘Guinness World Records’ a matsayin wanda ya fi kowa ne mai aski dadewa a duniya.

Anthony wani lokaci yakan jira masu zuwa a yi musu aski, yayin da har yanzu yake da kwarin yin askin.

Anthony yana da cikakkiyar koshin lafiya kuma bai shan kayan maye ko taba ta yadda za ta yi masa illa. Yadda yake gudanar da sana’arsa shi ne, a duk  mako yana bude shagonsa na kwana biyar yayin da yake yin aski na sa’o’i takwas a tsaye duk rana. Ya kuma bambanta da sauran masu sana’ar saboda yadda yake gudanar da ayyukansa.

Har yanzu hannunsa bai rawa idan ya rike kilafa duk tsufarsa yana yi wa jama’a aski kamar ba tsoho ba.

Anthony ya ce, bai tunanin nan gaba zai yi murabus daga sana’arsa.

Daya daga cikin abokin huldar Anthony, Chris Dunne, wanda ya bude shagon aski shekara hudu da suka gabata ya ce, Anthony Mancinelli ne kadai da ya sani wanda ya shahara a fannin saisaye suma, ba kamar sauran wanzamai ba.

Anthony Mancinelli ya kara da cewa, tun ina da shekara 11 nake sha’awar sana’ar aski, saboda ba na sha’awar in zauna a gida ba tare da yin komai ba. Har yanzu duk lokacin da nake yin wannan sana’ar ina ji kamar lokacin da nake da kuruciya ce.

Dan Anthony Mancinelli mai shekara 81mai suna Bob ya bayyana wa kafar labarai ta Times: cewa, “Anthony Mancinelli yana taimaka wa sa’o’insa lokacin da suka zo yin aski shagonsa musamman wajen zaunar da su a kujera.