✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Dattawa ta yi watsi da zangon mulki daya na shekara shida

Majalisar Dattawa ta fara tattaunawa kan rahoton kwamitinta kan gyaran tsarin mulkin 1999, inda mafi rinjayen sanatoci suka nuna adawa da kudirin da ke neman…

Majalisar Dattawa ta fara tattaunawa kan rahoton kwamitinta kan gyaran tsarin mulkin 1999, inda mafi rinjayen sanatoci suka nuna adawa da kudirin da ke neman a mayar da mulki ya zamo zango daya na tsawon shekara shida ga Shugaban kasa da gwamnoni.
A ranar 5 ga Yuni ne Kwamitin Gyaran Tsarin Mulki na majalisar a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Sanata Ike Ekweremadu, ya mika rahotonsa ga zauren majalisar, inda ya hana Shugaba Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo da dukkan gwamnonin da keg ado shiga zaben neman mulki na zangon shekara shida da aka gabatar a gyaran da aka yi wa tsarin mulkin.
Hanin na kunshe ne a karkashin batu na 12 na rahoton kwamitin da ke neman a cire sashi na 137 na tsarin mulkin wanda ya ce, “Duk mutumin da ke rike da mukamin Shugaban kasa ko Mataimakinsa kafin yin wannan gyara ga sashi na 135 da na 136 na tsarin mulki bai cancanci ya tsaya takarar neman mukamin na zango daya na shekara shida ba.”
Kamar Shugaban kasa, gwamnoni masu ci, ciki har da wadanda suke zangonsu na farko an haramta musu tsayawa takara don yin zango daya na shekara shida a karkashin sabuwar dokar kamar yadda batu na 8 da ke neman canja sashi na 180 na tsarin mulkin.
Mafi yawan sanatocin da suka yi magana a zaman majalisar na ranar Talatar da ta gabata sun yi adawa da shawarar, inda suka bayyana ta da “ta saba wa dimokuradiyya” kuma tana iya karfafa almundahana domin Shugaban kasa da gwamnoni ba za su ji tsoron sake neman zabe ba.  
Sanata Cleber Ikisikpo (PDP, Bayelsa), wanda ya fara magana ya ce, “Ban amince da batun zango daya na shekara shida ba, ya saba wa dimokuradiyya. Kuma zai karfafa almundahana saboda Shugaban kasa zai ji cewa yana da zango daya ne kawai, don haka zai tafka almundahana.”
Shi kuwa Sanata Ahmad Ibrahim Lawan (ANPP, Yobe), ya bayyana shawarar ce da “kiran asara da jawo jangwam da tado hautsini kuma ya saba wa dimokuradiyya….”
Shi kuwa Sanata Adamu Gumba (PDP, Bauchi) cewa ya yi, “ Jama’ata sun yi fatali da zango daya na shekara shida, kuma ina jin ya kamata mu yi watsi da shi.”
Majalisar har wa yau ta yi watsi da kudirin da ke neman a rika ba tsofaffin shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa fansho har karshen rayuwarsu, inda sanatocin suka ce mutanen mazabunsu sun ce ba su yarda da hakan ba.  
Sannan sanatocin sun yi watsi da yunkurin janye kariya ga Shugaban kasa da Gwamnoni daga cikin tsarin mulkin, kuma sun nanata cewa a soke Asusun Hadin Gwiwa tsakanin Jihohi da kananan Hukumomi, baya ga Sanata Gbenga Ashafa (ACN, Legas), wanda ya nemi a ba Legas matsayi na musamman tare da watsi da ’yancin kananan hukumomin.