✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Sakkwato ta amince da kwamishinonin da Tambuwal ya aike mata

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da sunayen kwamishinoni hudu da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aike mata don tantance su. Amincewar ta biyo bayan…

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da sunayen kwamishinoni hudu da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aike mata don tantance su. Amincewar ta biyo bayan kudirin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar,  Alhaji Garba Bello Yabo ya nema bayan tantance kwamishinonin da kwamiti ya yi.

 Alhaji Bello Yabo ya ce mutanen da za a bai wa mukaman suna da kima da jajircewar da za su iya rike mukaman a kowane fanni aka sanya su. “Mutanen za su taimaki Gwamna Tambuwal ga aikinsa a Majalisar Zartarwa ta Jiha har a cimna manufa mai kyau,” inji shi.

Shugaban Majalisar, Alhaji Salihu Maidaji ne ya jagoranci zamanta, inda ya nemi a amince da kudirin shugaban masu rinjayen kuma aka amince. 

Kwamishinonin sun hada da Farfesa A’isha Madawaki Isah wadda za ta kasance mace ta biyu a Majalisar Zartawar Jihar, sai Alhaji Ahmad Barade da Alhaji Garba Tsitse da Alhaji Bello Ambarura wanda ya ajiye aiki kwanaki kadan a matsayin Babban Sakatare kafin ya samu wannan mukami.