✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makiyan Buhari ne ke yada karyar cewa kuri’ar ’yan Izala kadai za ta ba shi nasara – Sheikh Kabiru Gombe

A makon jiya ne wasu kafofin sada zumunta suka fitar da wani labari da ke cewa Babban Sakataren Kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Muhammad Kabir…

A makon jiya ne wasu kafofin sada zumunta suka fitar da wani labari da ke cewa Babban Sakataren Kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya ce kuri’un ’yan Izala kadai za su iya ba Shugaba Muhammadu Buhari nasara a zaben bana, don haka ba ya bukatar kuri’ar ’yan Darika. Aminiya ta zanta da shi inda ya nesanta kansa daga wannan labari, ya ce makiyan Buhari ne suka kirkiro wannan labari na karya kuma suke yada shi don wata manufa tasu:

An ruwaito ka a wata kafar sadarwa cewa ka ce kuri’ar ’yan Izala kadai ta isa bai wa Shugaba Buhari nasara ba sai ya samu ta ’yan Darika ba, kuma wata jarida ta buga hakan, mene ne gaskiyar wannan magana?

Kamar yadda ka ji wannan labari ko ka gani, ni ma haka na ji ta. Kuma ban taba ganin jaridar da ake kira Madubi ba da aka ce ta ruwaito labarin. Kuma ta fadi jawabin ne ba tare da fadin inda na ambaci haka ba ko inda suka samo labarin ko a wane masallaci ko gari. Hira suka yi da ni, ko a mimbarin wa’azi suka dauki maganar?  Har zuwa yanzun nan ba mu samu amsarsu ba. Abu na biyu mun kalubalance su ta kafar sadarwar sada zumunta kamar yadda muka gan su ta kafar, don ba mu san daga ina suke ba, cewa su sako muryata inda na ambaci haka koda a wajen hira ce ko a tadi ko a kaset na bidiyo, amma sun gagara yin haka. Sannan batun a dauko wani hotona ko wani labari a danganta ni da shi a facebook ko ire-irensa, ba a yau aka fara yi min irin wannan sharri ba. Saboda haka wannan bai girgiza ni ba ko ya ba ni mamaki ba. Wani abin da ya kamata a yi la’akari da shi a kai shi ne, duk wanda ya karanta bayanin ya san ba ta mai kaunar Shugaba Buhari ba ne. Saboda duk wanda ke kaunarsa har ya kai ga ayyana goyon baya gare shi ba zai taba yin wannan aika-aikar ba, saboda kowa ya sani ana iya cin zabe da rinjayen kuri’a daya kuma ana iya rasa shi da kuri’a daya. Ashe ke nan mu ne ya kamata mu rarrashi jama’a tare da jawo su a kan su zabe shi, ba mu nemi korarsu ba mu ce a bar mu mu kadai. Wannan kadai ya kamata a gane cewa makiyanmu ne da  makiyansa da ma kasar baki daya suka kirkiro wannan magana. Ba mu san inda suke ba bare mu tunkare su illa dai mun fitar da maganar ta kafarmu ta sada zumunta ta JIBWIS mun karyata su tare da kalubalantarsu a kai.

To me ya sa kuka fito kuka ce a zabi Shugaban Kasa Buhari?

To alhamdulillahi kamar yadda ka tambaya, dalilai da yawa ne suka kai Kungiyar Izala ta fito karara ta bayyana goyon bayanta ga sake zaben Buhari, wanda hakan ba al’adar kungiyar ba ce a lokacin da ya tsaya takara a lokuta daban-daban. Sai dai a wannan karon mun fahimci akwai shubuha (abubuwa masu rudarwa) masu yawa da suka shigo cikin wannan zabe na bana. Idan ka dubi zaben da ya gabata, takara ce a tsakanin Musulmi dan Arewa da wanda ba Musulmi ba dan Kudu. To a irin wancan ba ka bukatar ka yi rubutu da manyan bakake kafin al’umma su fahimci ina aka dosa, karatun a fili yake. Abu na biyu a wancan karon ba a samu gamayyar makiya Najeriya da suke ganin sai sun raba ta sai sun kirkiro wata kasa a cikinta mai suna Biyafara ba. A wancan siyasa da aka yi ba su fito karara ba suka nuna maitarsu tare da fada da gaskiya a fili irin na wannan karo ba. Kowa ya ga irin tarurrukan da suke yi a yanzu da kuma sa albarka ga dattawansu da aka sani da akidar raba kasar nan, duk da dai cewa akwai masu hali nagari da muka sani da kyakkyawar manufa a cikinsu. Bayan nan ba a taba samun wani zabe ba da ’yan Shi’a suka fito karara tare da nuna kiyayya da maitarsu a fili na sai sun kawar da shugaba mai ci, irin na wannan karo ba. Na san a lokacin da Goodluck yake Shugaban Kasa sojoji sun kai musu hari a Zariya har aka kashe wadansu ’ya’yan jagoransu amma duk da haka ba su nuna gaba da niyyar yakar wancan gwamnati ba irin na wannan lokaci na gwamnatin Buhari ba, wannan ke nan. Sannan a daya bangaren an samu gamayya na taron dangi na wadansu da aka san su da munanan manufofi ga kasar nan da suka fito karara suka nuna inda suke, amma shi Musulmi sai a yaudare shi a ce masa ai gaba dayan mutane biyun Musulmi ne saboda haka a dauke su gaba daya abu daya ba tare da nuna wariya a tsakaninsu ba, a lokacin da gaba dayan makiyansa sun nuna su ga nasu. Ka ga ke nan ya zama dole shi ma Musulmi idan ya san abin da yake yi ya tsaya ya taimaki kasarsa ya taimaki al’ummarsa tare da samo wa kansa wanda zai yi masa adalci ya yi wa sauran al’umma kasa adalci, kuma dama haka addinin Musulunci ya ce. Wani abu da zai ba ka mamaki shi ne a cikin dukan wadanda suka ayyana goyon bayansu ga wannan Shugaban Kasa babu wanda ya dame su sai na kungiyar Izala, alhali kungiyar Izalar nan kungiya ce ta addini, siyasar nan kuma wani bangare ne na addini, saboda bangare ne da ke da alaka da rayuwar al’ummar Musulmi. Duk wanda zai dau tarihin Izala sai ya danganta ta da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Sheikh Abubakar Gumi ya wayar da kan mutane a kan cewa siyasa tana da alaka da addini. Allah Ya umarci Manzon Allah (SAW) Ya ce duk rayuwarsa ya ba Allah baya ga sauran abubuwa da aka sani kamar Sallah da sauransu. Wannan ya hada harda addini da mu’amala da kuma shugabanci, ita kanta kalmar siyass ai kalma ce ta Larabci.

Akwai masu ra’ayin cewa bai kamata malamai su rika sa baki a harkar siyasa ba, na baya-bayan nan shi ne wani fitaccen dan siyasa daga Kano, me za ku ce?

Idan a ka ce kada malamai su yi magana a kan siyasa abin da ake nufi shi ne a bar jahilai kadai da ta cewa a lamarin. Ke nan jahilai ne za su zaba mana shugaba wanda idan ya hau mulki dole su malaman nan su kasance a karkashinsa. An yarda karuwa ta sa baki a kan wanda zai yi mata adalci an yarda da dan daudu, malami kadai ne ba a yarda ya sa baki ba, alhali shi ne ya san yadda Manzon Allah (SAW) ya tafiyar da shugabanci ya kautata wa Musulmi da wanda ba Musulmi ba. Shi mai wannan magana da ke cewa bai kamata malamai su sa baki ba, shi me ya ba shi hurumin ya sa baki a siyasar, ai saboda shi dan Najeriya ne. Shin a tsarin mulkin kasa akwai inda aka ce malami kada ya sa baki a siyasar c?. A kur’ani dai ko Hadisi mun san babu, koda yake ya ce shi jahili ne bai san addini ba. Yanzu tambayar da za mu yi masa ita ce ya kawo mana hujja a dokar kasa da ake amfani da ita inda aka hana hakan. Mu dai a iya saninmu masu mutunci da masu sani su ne suka fi cancanta su sa baki a lamarin saboda su ne suka san siffofin da Allah (SWT) da ManzonSa (SAW) su ka bayar a kan mai adalci. Wata tambaya da zan yi ita ce shin wannan fatawar ta tsaya ne a kan malaman Musulunci kawai ko har da na Kirista. Idan har da na Kirista to Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo malamin addini ne ko siyasar ce kawai ya sani? Ga Rabaran daban-daban ko fasto da suka yi Gwamna, akwai su a ministoci da kwamishinoni da sauran matakan shugabanci, ka ga ke nan bai yi wa nasa al’ummar adalci ba. Kungiyar ACF ta Arewa da ke sa baki al’amuran siyasa shin babu masana addini a cikinsu ne, yana nufin jahilai ne su gaba daya? Ba ya ga nan kafin Izala ta fito ta yi bayani wadansu malamai da dama sun fito sun yi bayani a kan siyasar nan ciki har da wanda ya fito ya tsine wa duk wanda ya goyi bayan Buhari kuma a kan mimbarinsa na wa’azi amma shi wannan dan siyasar ba a ji ya fito ya soki lamarin ba, sai na Izala wadda ba ta zagi kowa ba, ba ta soki kowa ba, ta dai yi magana ce kawai ga mabiyanta wanda shi bai taba danganta kansa da su ba, sai a kanta ne kawai zai fito ya yi magana. Wannan jahilci ne kuma ya bayyana wa duniya wautarsa kamar yadda shi da kansa ya bayyana cewa shi jahilin ne. Wannan ba karamin kuskure ba ne musamman ga irinsa wanda ya fito yake neman ya shugabanci al’umma da kasa baki daya wanda akidarsu ita ce malami bai da hurumin da zai iya yin magana a kan harkar shugabanci, aikinsa kawai da kuma huruminsa a wajensu shi ne su koma gefe su yi ta yi musu addu’a, har ma yake tabbatar wa duniya cewa ya tara yara wadanda zai iya tura su su yi kowane irin ta’addanci ga wanda ya umarce su. Sai dai kawai mu gode wa Allah da Ya fara tona asirin irin wadannan ’yan siyasa, kuma da sannu al’umma za su gane su, ga su ga al’ummar. Allah dai Ya yi umarni a cikin Alkur’ani ga jama’a su koma gare Shi da ManzonSa, a duk lokacin da aka samu sarkakiya a cikin wani lamari. To a yanzu da Manzon Allah (SAW) ba ya nan, wajen jahilai za a je a nemi fatawar ko kuma wajen malamai masana Kur’ani da Hadisin da Manzon Allah ya bari.

Me ya sa kake jin ake danganta ku da irin wadannan abubuwa?

Dalili daya ne bai rasa nasaba da ganin irin tasirin da bayananmu ke yi a kan al’umma a duk lokacin da muka fitar, kuma hanya daya tak da za a bi a yi fada da mu ita ce ta irin wadannan hanyoyi, babu dama su fito gaba-da gaba su fuskance mu sai ta irin wadannan hanyoyi na sharri da kirkira a rubuta a shafin sada zumunta a yada. A irin wannan tasirin da nake bayani, daga lokacin da muka bayyana wannan matsaya tamu wasu karin kungiyoyi ke ta fitowa suna cewa su ma sun goyi bayan Buhari, wannan abin farin ciki ne muna godiya. Allah Ya nuna mana wannan zabe lafiya a gama lafiya.