Search
Subscribe
Malama marar hannuwa na amfani da baki wajen yin rubutu ga dalibai

Malama marar hannuwa na amfani da baki wajen yin rubutu ga dalibai

Wata malamar makaranta mai suna Enyonam Louisa Esi, da ba ta da hannuwa tana ci gaba da gudanar da wasu ayyukanta na yau gobe. An yi ta yada hotunanta rike da alli ko alkalami a bakinta tana rubutu a jikin allon bango ga dalibanta.

Madam Enyonam, malama ce a Makarantar Adoagyiri R/C da ke garin Kasoa a kasar Ghana, inda rayuwar ta canja akalar masu fama da nakasa bayan wallafa hotonta tana rike da alli a baki tana koyar da dalibai inda aka yi ta yada wadannan hotuna tun bara.

Hoton malamar ya yi matukar tasiri ga masu bibiyar shafukan sadarwar zamani lokacin da take koyarwa tare da alli a bakinta sanadiyyar rashin hannun da take da shi.

Madam Enyonam, ta ce rashin hannuwanta bai hana ta koyar da dalibai ba, hakan ya sa ta san yadda za ta iya amfanin da bakinta wajen yin rubutu da dabarun koyar da daliban.

Malamar dai tana kokarin koyar da daliban ne duk da nakasa da take tattare da ita a matsayinta na malamar makaranta kuma a hakan take bai wa dalibanta ilimi ba tare da nuna gazawa ba.

Enyonam, tana ba da ilimi kamar yadda kowane malami ke ba da darasi ga dalibansa, kuma wannan malama tana koyar da darasin da ke koyar da yadda mutum zai iya zama shugaba (shugabanci), duk da yanayin kalubalen da mutum zai iya fuskanta har zuwa matakin samun nasara.

Duk da yanayin mutum zai iya cika burin rayuwarsa ta hanyar fahimtar abin da zai iya aikatawa.

A wani lokaci wadansu nakasassu ba su iya bari a bar su a baya don haka suke kokarin nuna bajintarsu duk inda suka samu kansu, ta yadda wadansu ke tunanin nakasassu ba su iya gudanar da wasu abubuwa.

Yadda Madam Enyonam, ke gudanar da rayuwarta zai kara wa nakasassu karfin gwiwa wajen gudanar da harkokinsu na yau da gobe, hakan zai iya kowa ci gaba a cikin al’umma.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin