✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malaman Saudiyya sun yi zanga-zangar adawa da tukin mata

Manyan malaman addini 150 ne suka yi zanga-zangar adawa da ba mata damar tukin mota, a gaban fadar Sarkin Saudiyya, ranar Talatar da ta gabata.…

Wasu daga cikin manyan malaman SaudiyyaManyan malaman addini 150 ne suka yi zanga-zangar adawa da ba mata damar tukin mota, a gaban fadar Sarkin Saudiyya, ranar Talatar da ta gabata. Wasu daga cikin manyan malaman sun zargi kasar Amurka da yunkurin tabbatar wa mata ’yancin tuka mota nan da washegarin Asabar. Domin a cewarsu, ‘an tattara sa hannun mutum dubu 16,’ na jerin masu fafutikar tukin mata a kasar.
Kuma me ya sa aka yi amfani da watan Miladiyya bana Larabci ba?” a cewar daya daga cikin malaman da ke adawa da tukin mata, Sheikh Nasser el-Omar, inda ya yi nuni da cewa kalandar hijirar Musulunci ta saba wa ta Gregori, wadda yammacin Turai ke amfani da ita.”
“Wannan na nufin Amurka ta tsara yadda za a yi fafutika,” a wani sharhi da ya yi wa shafin sadarwa na Akhbar 24. Duk da cewa dokokin hanya a Saudiyya ko shari’ar Musulunci ba su fito karara sun hana mata tuki ba, amma ba a bai wa mata lasisin tuki a kasar, koda sun nema.

 

 

 

 

 

 

 

…Matan Saudiyya na shawagi a sama

Matan Saudiyya da aka hana su tuka mota, sun koma koyon tukin kananan jiragen sama, wadanda ake harbawa cikin iska na “gilders.” Don haka kungiyar masu bayar da horon tukin kananan jiragen da ke Jedda (Saudi Abiation Club), ta fara bayar da hayar irin wadannan jirage ga masu bukata. Wanda duk ke son mallakar irin wannan dan karamin jirgi, sai ya tanadi riyal dubu 37 zuwa Riyal dubu 400 (daidai da Naira miliyan 16), kamar yadda jaridar Al-Madina ta ruwaito.
Jaridar ta tura wakilinta zuwa harabar inda kungiyar matuka kananan jirgin ke gudanar da harkokinsu a kan titin Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah, ga wadanda ke samun horo ba tare da wata tsangwama ba.
daya daga cikin matan da ke tuka irin wadannan kananan jirage, mai suna Taghreeed ta ce shawagi a sama na sanya annashuwa, ta yadda mutum zai manta da abin da ke faruwa a kasa: “Mutum zai ji dadin kallon duniya daga sama da kogi, ya kuma shaki iska mai dadi, ba tare da an musguna masa ba,” inji ta.
Amal, wata mai samun horo, ta bayyana cewa shawagin sama wasa ne da ya fi dacewa da mata a Saudiyya. Kudin samun horon tuka kananan jirage ya kai riyal 800 (Naira dubu 36) a kowace sa’a, a cewar Daraktan Makarantar, Muhammad Al-karni: “Mafi karancin lokacin koyo da mutum ke bukata bai wuce sa’o’i 10 ba, amma wasu na bukatar har sa’o’i 30,” inji shi.