✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malawi ta dakatar da sanya huluna da rigunan lauyoyi saboda zafi

Yanayin zafin da ke karuwa a kasar Malawi, ya tilasta kotun tsarin mulkin kasar bayar da umarnin dakatar da bukatar nan ta lallai sai lauyoyi…

Yanayin zafin da ke karuwa a kasar Malawi, ya tilasta kotun tsarin mulkin kasar bayar da umarnin dakatar da bukatar nan ta lallai sai lauyoyi da alkalai sun sanya riguna da hulunan shari’a na al’ada a duk kotunan kasar.

Ma’aunin yanayin zafi a wasu yankunan kasar da ke Kudancin Afirka, ya kai digiri 45 (113 Fahrenheit) a wannan mako mai karewa, kamar yadda hukumar kula da yanayi ta kasar ta nuna.

Malawi, wacce rainon Turawan Birtaniya ce, har yanzu tana bin tsarin shari’a irin na uwargiyarta Birtaniya sau-da-kafa – ta hanyar amfani da huluna tare da manyan rigunan lauyoyi da sauran masu shari’a.

Sai dai Chikosa Silungwe, daya daga cikin lauyoyin kasar ya fada a Lilongwe babban birnin kasar cewa, yanayin zafi a kasar yana haifar da babban kalubale a ayyukan kotunan kasar.

“A takaice, lamarin na gaskiya ne. Yanayin zafin da ake fama da shi a wannan mako ya nuna cewa saka wannan suturar ba ya da dadi ko kadan,” kamar yadda ya bayyana a hirar tarho da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Agnes Patemba, Babbar Magatakardar Babbar Kotun Kasar kuma kakakin bangaren shari’ar kasar, ta bayyana cewa dage sanya wannan sutura da ya fara aiki shekaranjiya Laraba, ba na dindindin ba ne.

“Akwai karuwar yanayin zafi kuma hakan ya tilasta kotu ta yi watsi da wannan sutura. Kuma hakan ba shi ne karon farko da ake dakatarwar ba,” inji  Patemba.

Babbar Kotun Malawi na sauraran wata karar da sashen ’yan hamayyar kasar suka shigar inda suke neman ta soke zabubbukan kasar da aka gudanar a bana, bisa abin da suka kira yana cike da kura-kurai.

Ma’aikatar Lafiya ta Kasar ma ta fitar da wata sanarwa inda take gargadin jama’a game da illolin da ke tattare da karuwar zafi a kasar tare da kiran jama’a su dauki matakan kandagarki.