✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Fasa Bututun Mai Sau 9,000 A Shekara 1 —NNPCL

A cewarsa, daga 2022 zuwa yau, kamfanin ya lalata haramtattun matatun mai guda 6,465.

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya ce an fasa bututun danyen mai sau 9000 cikin shekara daya a Najeriya, inda ya koka kan yadda ake yawan samun matsalar a kasar nan.

Kyari ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin wata ziyara da kwamitin Majalisar Wakilai kan satar mai ya kai masa a hedikwatar kamfanin da ke Abuja. 

A cewarsa, daga 2022 zuwa yau, kamfanin ya lalata haramtattun matatun mai guda 6,465, da aka gina ba bisa ka’ida ba. 

“Mun kuma balle haramtattun bututun mai da aka makale a jikin na NNPCL 4876 daga cikin 5,570 da muka gano.” 

Sai dai ya nuna damuwarsa kan cewar har yanzu kamfanin ba shi adadin haramtattun bututun da ake satar danyen mai da su. 

Kazalika, ya kara da cewa: “Wasu daga cikin nau’in satar da muke gani,  idan ba mutum ne ya gani da idanonsa ba, to ba zai yarda ba. Lokacin da muka cire wani bututu da aka makale a jikin na NNPCL ɗaya, washegari za ka ga an maye gurbinsa da wani.

“Galibin wadannan wuraren da ake fasa bututu mai, ba su wuce mita 100 ba daga garuruwan al’ummar yankin ba; wasu ma ba su kai mita 100 daga hedikwatar kamfanin ba.” 

Kyari, ya ce ana yin wadannan munanan ayyuka ne ba tare da tsoro ko shakka ba. 

Ya kara da cewa wannan mummunar sata da ake yi ba dare ba rana ta sa ba za a iya tabbatar da abin da za a iya  samarwa washegari ba.

Ya kara da cewa babban abin da ya fi daukar hankali shi ne batun tsaro, inda ya ce kamfanin NNPC ya yi kokarin dakile matsalar fasa bututun mai ta hanyar sanya dukkan hukumomin tsaro cikin runduna guda. 

Ya ce, “Muna da karfin samar da danyen mai sama da ganga miliyan biyu a kowace rana.” 

Shugaban Kwamitin na Majalisar Wakilan, Alhassan Ado-Doguwa, ya ce,  sanin kowa ne gudanar da harkar mai ta bututun mai da iskar gas a Najeriya babban aiki ne da ke cike kalubale. 

A cewarsa abu ne mai wahalar gaske a yi sati guda ba tare da rahoton satar danyen mai ba.

A gefe guda ya ce rashin sanin halin da ake ciki a tashoshin fitar da danyen mai na Najeriya abin damuwa ne.

Ya bayyana cewa babu tantama Najeriya tana fama da matsalar satar danyen mai da fasa bututun mai da yawa, inda ya ce galibin satar na faruwa ne a yankin Neja Delta.