✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman auduga 189 a Sakkwato sun samu tallafin Gwamnatin Tarayya

Manoman auduga 189 a Jihar Sakkwato sun amfana da shirin noma na Gwamnatin Tarayya a matakin farko na wadanda aka fara ba rance. An raba…

Manoman auduga 189 a Jihar Sakkwato sun amfana da shirin noma na Gwamnatin Tarayya a matakin farko na wadanda aka fara ba rance. An raba wa manoman audugar rance buhunan taki bakwai-bakwai da buhun irin auduga daya da maganin kwari daban-daban da za su taimaki shukar ta samu bunkasa yadda ake so.

Aminiya ta zanta da wadanda suka samu tallafin kan fatarsu ga shirin na noman auduga, inda Iliyasu Bara’u wanda ya fito daga karamar hukumar Isa, daya daga cikin kananan hukumomin da aka ware domin gudanar shirin farfado da noman auduga a jihar ya ce su 13 ne suka zo daga karamar hukumar don su karbi kayan noman bayan an tantance su a karamar hukumar.

“Da farko mun cika fom da muka biya Naira 500, yanzu an kira mu a ba mu tallafin bashin kayan noman auduga an ba mu buhun taki bakwai da irin auduga buhu guda da maganin kwari. Kafin a mika wa mutum wadannan kayan sai ya ba da Naira 4,500. Wannan kudin daban yake; ba ya cikin tallafin kaya. Muna fata wannan shirin ya ci gaba don a bunkasa noman auduga a Najeriya,” inji shi.

Alhaji Abu Sala daga Karamar Hukumar Tambuwal ya ce “Kungiyoyinmu na manoma sun kai 20; ni mamba ne a kungiya daya daga cikinsu, na biya Naira dubu hudu kudin bude asusun ajiya na banki da sauransu ga kungiyarmu; an ba ni tallafin kayan noma zan je in yi noma kamar yadda na saba yi tsawon lokaci.”

Bello Garba Isah yana cikin wadanda suka karbi kayansu a matakin farko ya ce an san su ne a manoman auduga suna nomanta sosai a wajensu an tantance su a farko sun bayar da Naira 500 na fom yanzu sun karbi kayan noma bayan sun bayar da Naira 4.500.

“An gaya mana yadda kudin suke Naira dubu 2 na uwar kungiya ce, za a bai wa lebarori 500, a bude asusun ajiyar banki da Naira dubu daya,” inji Bello Garba.

Mukhtar Sanusi Bargaja ya ce yankinsu da ke fama da masu tayar da kayar baya lamarin ya yi sauki sosai sun ci gaba da nomansu duk da akwai kauyuka kusan 73 da suka tashi gaba daya.

“Bayan wannan tallafi na noman auduga na taba samun tallafin noman albasa. An ce wai ga hasashe za mu biya kudin kayan da aka ba mu kan Naira dubu 72, za a saka mana kudi a asusunmu Naira dubu 150, ko yaya ne dai sai mun gani,” inji Bargaja.

Musa Lumu Gwadabawa Shugaban Kungiyar Manoman Auduga ta Jihar Sakkwato ya ce: “Manoma 189 ne za su amfana; da farko za a yi zagaye na biyu ba mu san ko mutum nawa ne ba sai an kawo sunayensu domin mun tura mutane sun fi 2,500.”

“Kudin kayan noma da wadanda manomi zai kashe har zuwa auduga ta girma a cire, an kiyasta jimillar Naira dubu 170, an yi yarjejeniya da manomi wadanda suka ba shi kaya su zai sayar wa auduga. An ce kowa ya bude asusun ajiya wuri daya ne don saukin mu’amala,” inji Musa Lumu.