Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Masha Allah an yi zabe lafiya gwargwadon zarafi

Cikin ikon Allah da kudurarSa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya tsaya takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar APC shi ya yi nasarar lashe zaben bana da kuri’a miliyan 15 da dubu 191 da  847 (15,191,847), adadin da ya kai kashi 56 cikin 100, daga yawan kuri’un da aka kada. Yayin da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya zo na biyu da kuri’a miliyan 11 da dubu 262 da 978 (11,262,978), wato kashi 41 cikin 100, na yawan kuri’un da aka kada a zaben Shugaban Kasa da  na Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar Asabar da ta gabata. Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), kuma Babban Baturen Zabe na Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana sakamakon zabe a kusan wayewar garin shekaranjiya Laraba a Abuja. Jam’iyyu 73, suka shiga takarar, kuma daga sakamakon da ake da shi yanzu sauran jam’iyyu 71, su suka tashi da kashi 3 cikin 100, na yawan kuri’un da aka kada.

Wannan shi ne karo na farko tunda aka fara mulki a wannan Jamhuriyar ta Hudu a 1999, kimanin shekara 20, aka taba samun ’yan takara masu yawa a cikin zabubbukan kasar nan da kuma yawan masu kada kuri’a. Alal misali a bana an samu ’yan takarar Majalisar Dattawa 1,904, da suka fafata don neman kujera 109, na majalisar. Akwai kuma ’yan takara 4,680, da suka kece raini don neman kujerun Majalisar Wakilai 360. Sai masu kada kuri’a miliyan 80 da dubu 4 da 84, wanda shi ne adadi mafi yawa na masu kada kuri’a da aka taba samu. Kamar yadda ’yan takarar shugabancin kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa suka karu a sanadiyar karuwar jam’iyyun siyasa da Hukumar INEC ta yi wa rijista a wannan karo, su ma masu kada kuri’ar sun karu da mutum  miliyan 15, wadanda a bana suka cika shekaru 18 da haihuwa kamar yadda tsarin mulki ya tanada ko kuma sai a wannan karon suka ga damar su yi rajistar kada kuri’ar.

ADVERTISEMENT

Sakamakon zaben Shugaban Kasar kamar yadda Farfesa Yakubu ya bayyana shi ya tabbatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu lashe zaben bayan ya zo na daya a jihohi 19, yayin da Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, ya zo na daya a jihohi 17, da Babban Birnin Tarayya Abuja kuma ya zo na biyu. A kusan dukan jihohin Arewa 19, Shugaba Buhari ne ya zo na daya da mafi rinjayen kuri’u, in ban da a jihohin Adamawa mahaifar Alhaji Atiku da Taraba da Filato da Benuwai da kuma Birnin Tarayya, Abuja.

A jihohin shiyyar Kudu maso Yamma inda Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya fito, Shugaba Buhari ya zo na daya a jihohin Legas da Ogun jihar tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo da kuma Ekiti da Osun, ya zo na biyu a jihohin Oyo da Ondo. A dukan jihohin shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, har har da Jihar Edo mahaifar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Kwamared Adams Oshiomhole, Shugaba Buhari ya zo na biyu ne. Zuwan Shugaba Buhari na biyu a wadannan shiyyoyi biyu a wannan zaben ko kusa bai zama wani abin mamaki ba, kasancewar tunda aka fara mulkin farar hula wadancan jihohi 11, suna tare da Jam’iyyar PDP, kuma dadin dadawa a wannan karon Jam’iyyar PDP ta dauki mukamin Mataimakin Shugaban Kasa sukutum ta ba Mista Peter Obi tsohon Gwamnan Jihar Anambra daga shiyyar Kudu maso Gabas. Mukamin da ba ta taba samu ba daga wata babban jam’iyya a wannan zubi. Su kuma dama mutanen shiyyar Kudu maso Kudu ko Neja Delta duk da tsirarun kabilu ne a Kudancin kasar nan amma dama can sun fi alakanta siyasarsu da kabilar Ibo da suke makwabtaka.

ADVERTISEMENT

Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP, bisa ga nazari mai zurfi a iya cewa sun taka gagarumar rawa a cikin zaben ta la’akari da irin yadda Atiku ya bar Jam’iyyar PDP dab da za su kammala zangonsu na biyu shi da Shugaba Obasanjo a shekarar 2007. Bayan nan ya yi ta yawo a cikin wasu jam’iyyu har zuwa shekarar 2014, ya sa hannu aka kafa sabuwar Jam’iyyar APC, daga baya ya nemi ya yi mata takarar Shugaban Kasa. A bara kuma ya sa kafa ya shure jam’iyyar ta APC ya yi wa jam’iyyarsa ta asali kome, har ta tsayar da shi dan takarar Shugaban Kasa a wannan zabe.

Wani abu kuma da masu nazari suke gani, shi ne irin cin amanar kasa da tambadar da dukiyar kasa da PDP ta yi wa arzikin kasar nan a mulkinta na shekara 16 ba kakkautawa daga 1999 zuwa 2015. Har yanzu wadansu ’yan kasa ba su yafe mata bar su sake zabenta. Sannan daga yadda aka gudanar da yakin neman zabe, wadansu masu muradin ganin an gyara kasar nan suna fargabar cewa muddin Alhaji Atiku ya yi nasara, ko shakka babu sace-sace da sama-da- fadi da dukiyar kasa da mayar da hannun agogo baya kan yakin da Shugaba Buhari ke yi da cin hanci da rashawa, duk gwamnatin Atiku za ta yi watsi da su, a koma gidan jiya.

Ko shakka babu kauna da soyayyar da Allah Ya cusa a zukatan akasarin talakawan kasar nan masu kada kuri’a a kan Shugaba Mahammadu Buhari, ita ta kai shi ga wannan nasara, amma ba wai don masu fada-a-ji na kasar sun so haka ba. Sanin haka a zukatan talakawan ya sanya bayan an bayyana shi da cewa shi ya yi nasara a zaben aka jiyo Shugaba Buhari yana nanata wa mutanen kasa cewa zai ci gaba da ayyukan da ya faro, wato na tabbatar da kawo tsaro da zaman lafiya da farfado da tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa. Ya kuma kamata a zangon na biyu ya kara waiwayar jihohin Arewa baki dayansu a kan ayyukan raya kasa, sabanin yadda ya mayar da karfinsa wajen malala ayyukan raya kasa a shiyyar Kudu maso Yamma, wato shiyyar da ta kunshi kabilar Yarbawa da danta yake Mataimakin Shugaban Kasa tun shekarar 2015.

Akwai rade-radi masu karfi da ke cewa Alhaji Atiku ba zai hakura ya karbi kaddara ba, wato zai je kotu. In ya je kotun ba laifi ba ne, don kuwa Shugaba Bahari tun a shekarar 2003, da ya fara takarar shugabancin kasar nan yake zuwa kotu har zuwa shekarar 2011, amma dai yin hakuri ya fi, ko don ma samun ci gaban dimokuradiyyar kasar nan.

Saura da me? Tun a cikin watan Satumba zuwa Oktoban bara da aka fara zaben cikin gida na fitar da ’yan takarar  da suka tsaya wa jam’iyyunsu takarar aka yi ta samu rigingimu da tashe-tashen hankula da suka rika haddasa asarar rayuka da jikkata jama’a a sassa daban-daban na kasar nan, amma dai babban abin jin dadi, in ban da rigingimun da aka samu a jihohin Legas da Ribas a lokaci da bayan wannan zabe, an yi zabubbukan lami lafiya har masu sa idanu na kasa da kasa suka yaba.