Da Dumi Dumi

Masu garkuwa da mutane su 6 sun shiga hannu a Bauchi

Kungiyar tsaro ta Danga reshen  Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, ta samu nasarar kama wadansu matasa shida da ake zargin sun addabi al’ummar yankin da fashi da makami da garkuwa da mutane.

Shugaban Kungiyar Danga a Karamar Hukumar Toro Alhaji Yusuf Abdullahi ya ce sun kama matasan  6 ne a garin Rinji da ke tsakanin Magama Gumau da Toro.

Ya ce matasan 6, sun hada da Agwom Azi da Usman Abdullahi da Jamilu Muhammad Aljan da Ayuba Bala da Ishaku Samson da kuma Garba Yakubu Maidaji.

Ya ce sun samu daya da bindiga da kuma wanda yake kera bindigogin da suke amfani da su wajen aikata fashi da garkuwa da mutane.

“Matasan a duk ranakun kasuwa a yankin suna tare hanya su yi wa mutane fashi. Za mu mika su ga ’yan sandan Toro don su don ci gaba da bincike,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya yi kira ga gwamnati da manyann kasa su ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai, don ganin an  magance matsalar tsaro a yankin.

Da yake zantawa da wakilinmu daya daga cikin matasan Agwom Azi, ya ce shi yana sana’ar walda ce a garin Rinji  Ya ce babu shakka ya hada baki da matasan inda suka zo wani shago da ke kallon gidansu da daddare suka yi fashi kuma suka tafi da yaran shagon biyu mace da namiji ’yan kabilar Ibo. Da gari ya waye ya hadu da daya daga cikin matasan, ya ciro Naira dubu 45 ya ba shi a matsayina nasa kason.

Ya ce ya aikata fashi da garkuwa da mutane a yankin.

Shi ma Usman Abdullahi ya ce yana zaune a garin Rinji. ‘‘Mun taba zuwa  hanyar Agware sau biyu muna tare mutane mu karbi kudadensu. Kuma mun taba zuwa mun fasa shaguna biyu mun kwashi kudade,” inji shi.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan lamari, Shugaban Riko na Karamar Hukumar Toro Alhaji Shehu Buba Umar ya mika godiya ga Allah kan wannan nasara da aka samu. Ya ce ganin yadda wannan matsala ta garkuwa da mutane da fashi da makami ta yi kamari, ganin wannan nasara da aka samu ta kama matasan ya sa ya kira taron dukkan masu ruwa-da-tsaki a yankin.

Ya ce taron ya samu halartar dukkan tsofaffin shugabannin karamar hukumar da tsofaffin kwamishinoni daga yankin da sarakuna da manyan malamai, inda suka tattauna tare baiw a juna shawarwari kan al’amarin.

Ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da hada kai da Kungiyar Tsaro ta Danga da Kungiyar ’Yan Banga na yankin da sauran jami’an tsaro don magance wannan matsala.

Ya yi kira ga sarakuna da  shugabanni da iyaye su tashi tsaye wajen koya wa matasa sana’a da kokarin tabbatar da tsaro a garuwan yankin.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti kan lamarin amma bai same shi ta waya ba.

Share